Shari'ar Bafarawa: Uba da da sun dage kan sai dai ayi shari'ar su daban-daban
Yayin da shari'ar tsohon Gwamnan jihar Sokoto na farko a wannan jamhuriyar, Alhaji Attahiru Bafarawa da kuma dan sa Sagir tare da kamfanin sa ta kara tasowa bisa zargin karkatar da wasu makudan kudaden gwamnati daga hannun tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Kanal Sambo Dasuki, sun dage kan sai dai ayi wa kowa tashi daban-daban.
A zaman babbar kotun dake a Maitama, garin Abuja, na kwanan baya ne dai aka yi fatali da bukatar su ta farko na cewar dole sai dai a raba shari'un daban-daban.

KU KARANTA: Hotunan wanda ya lashe kyautar muni sau 5 a duniya
Legit.ng dai ta samu cewa manyan Lauyoyin dake kare wadanda ake tuhumar ne dai suka bukaci a raba shari'ar saboda a cewar su hada shari'ar da akayi ne ma ke kawo wa shari'ar tarnaki musamman ma duba da yadda komai ya tsaya cak tun da aka fara a shekarar 2015.
To sai dai lauyan dake kara Rotimi Jacobs ya yi inkarin wannan kuduri na wadanda ake kara inda ya kuma bayyana cewa yin shari'ar a lokaci daya shine yafi dacewa kasantuwar dukkan laifukan nasu iri daya ne.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng