Madalla! Dangote ya karyar da farashin buhun simintin sa a kasuwar zamani
Labarin dake iso mana na nuni da cewa babban kamfanin nan dake samar da simintin gini a Najeriya mallakin shahararren attajirin nan daga Arewacin Najeriya watau Dangote ya karyar da farashin kudin buhun simintin sa bayan da ya shiga wata yarjejeniya da kasuwar nan ta zamani watau Jumia.
An dai sanar da wannan labarin mai dadi ne a yayin da aka gudanar da bikin saka hannun yarjejeniyar tsakanin kamfunnan biyu a Jihar Legas tsakanin wakilin Dangote Mista Chux Mogbolu da kuma shugabar ta Jumia Juliet Anammah.
KU KARANTA: Wayar salulu ta jefa wasu matasa gidan yari
Legit.ng dai ta samu cewa yanzu mutane zasu iya sayen buhunnan simintin da suka kama daga 300 zuwa sama masu nauyin kilo 50 a kasuwar zamanin ta Jumia a kan sabon farashin Naira 2,500 sabanin farashin sa a kasuwa.
To amma kuma dai wannan garabasar yarjejeniya ta nuna cewa za'a same ta ne a tsakanin garuruwan Legas, Abuja da kuma Fatakwal babban birnin jihar Ribas a halin yanzu kuma ba tare da biyan kudin mota ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng