Ina Masallacin nan wanda saira kiris ya ruguje? Toh wasu mutanen kirki sun yi hubɓasa, kalli hotunan sa yanzu

Ina Masallacin nan wanda saira kiris ya ruguje? Toh wasu mutanen kirki sun yi hubɓasa, kalli hotunan sa yanzu

Tuni dai an samu wasu Musulmai masu hubbasa, kuma masu yi don Allah sun bazama suna aikin sabunta ginin Masallacin nan da ya kusa faduwa, wanda hotonsa ya mamaye shafukan yanar gizo an tattare shi da Itace.

Rariya ta ruwaito wannan Masallaci a kauyen Indabo yake, cikin karamar hukumar Wudil din jihar Kano, kuma a yanzu haka wasu mutane da basu bayyana kansu ba su ruguza shi, sun sake ginawa har an kai linta.

KU KARANTA: Robert Mugabe yayi amanna da hambarar da gwamntinsa, ya nemi tafiya gudun hijira

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a baya dai jama’a da dama sun koka kan yadda ake Sallah a cikin wannan Masallaci das aura kiris ya rushe, a irin haka ne idan ya fado ya kashe mutane sai suce ai Allah ne ya kawo.

Ina Masallacin nan wanda saira kiris ya ruguje? Toh wasu mutanen kirki sun yi hubɓasa, kalli hotunan sa yanzu
Masallacin a da

Sau dayawa haka al’ummomi ke zaune kara zube, ba tare da sanin sune musabbabin wasu masifu dake tasowa a cikinsu ba, ba tare da sun yi wani yunkuri ko na minti daya ba don ganin sun magance faruwar hakan ba tun farko.

Ina Masallacin nan wanda saira kiris ya ruguje? Toh wasu mutanen kirki sun yi hubɓasa, kalli hotunan sa yanzu
Masallacin a yanzu

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng