An kafa sabuwar kungiyar addinin Krista a Kaduna

An kafa sabuwar kungiyar addinin Krista a Kaduna

- Mabiyan addinin Krista a arewacin kasar sun kafa wata sabuwar kungiyar, CNNC a jihar Kaduna

- Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya jagoranci taron

- Kakakin majalisar wakilai ya nuna damuwa game da rashin hadin kai tsakanin Kiristoci na arewacin kasar

Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara da kuma sauran Kiristoci da dama a jihar Kaduna, a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba suka kafa wata sabuwar kungiyar Krista mai suna “Congress of Northern Nigeria Christians” (CNNC), Kungiyar Kiristocin Arewacin Najeriya.

Wakilai daga jihohi 19 da ke arewacin Najeriya da birnin tarayya sun halarci taron.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , Gowon a taron ya gargadi wadanda suka kafa kungiyar CNNC cewa su nizanci abin da zai iya kawo baraka tsakaninsu da kungiyar Kirista ta kasa CAN a kan magance matsalolin da suka shafi Krista a yankin.

An kafa sabuwar kungiyar addinin Krista a Kaduna
Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon da shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Tsohon shugaban Najeriya, wanda ya jagoranci taron, ya bukaci Kiristoci a Arewa su hada kansu domin su yi magana da murya daya akan batutuwa da suka shafi zamantakewa ta gari a kasar.

KU KARANTA: Ana iya tsige gwamna Ganduje daga kujerarsa matuƙar bai naɗa babban Alkalin jihar Kano ba

Dogara, a cikin sakonsa, ya nuna damuwa game da rashin hadin kai tsakanin Kiristoci na arewacin kasar.

Ya ce, "Matsala tsakanin Krista a Arewa shine rashin hadin kai. Ina ƙaunar Allah da jawo hankalin al’umma zuwa bauta wa Allah? Babban abokin gaba na Ikilisiya da Kirista shine rashin biyayya".

Dogara ya yi alkawarin tallafa wa kungiyar don cimma burinta da manufofinta, ya kara da cewa mabiyan addinin Kristi su koyi yafe wa juna don samu yarda Allah.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng