Matar Cristiano Ronaldo ta haihu, an samu Ýa mace (Hoto)
- Fitaccen dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya samu karuwa
- Matar Ronaldo Georgina Rodriguez ta haifi ya mace
Fitaccen dan kwallon nan dake taka leda a kungiyar kasar sifaniya, Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya samu karuwa a daren Lahadi, 12 ga watan Nuwamba.
Gwarzon dan kwallon Duniyan na bana, Ronaldo, ya bayyana haihuwar ne ta shafinsa na kafar sadarwar zamani, Facebook, inda ya daura hoton budurwar tasa, Georgina Rodriguez tare da jaririyar a gadon Asibiti.
KU KARANTA: Guntun kashin dake tare da Sule Lamido ya ishe shi abin kunya – Fadar shugaban kasa
Ronaldo ya daura hoton tare da taken “Yanzun nan aka haifi Alana Martina, kuma Geo da Alana cuna cikin koshin lafiya.”
Legit.ng ta ruwaito a kwanakin baya ma sai da wata budurwar Cristiano ta haifa masa yan biyu, mace da namiji, wanda ya rada ma suna Mateo da Eva.
A yanzu haka Ronaldo yana yaya hudu kenan, da suka hada da babban dansa Cristiano Jnr, Matoe, Eva da kuma sabuwar jaririya Alana.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng