Yadda wani dan Najeriya ya ci na jaki a kasar Indiya
Wasu kafofin yada labarai a kasar Indiya musamman ma na sada zumuntar zamani sun yi ta nuna wani faifan bidiyo dauke da yadda wasu gungun yan kasar ta Indiya suke lakadawa wani dan kasar Najeriya dukan kawo wuka a babban birnin kasar, Delhi.
Haka ma kuma dai kamfanin dillancin labaran kasar mai suna ANI ya ambato cewa wasu mutane ne suka nadi faifan bidiyon a ranar 24 ga watan Satumban da ya gabata a cikin wannan shekarar.
KU KARANTA: Ronaldo na daf da kafa tarihi
Legit.ng dai ta samu cewa a cikin bidiyon an ga yadda yan kasar ta Indiya suka rika yiwa mutumin mugun bugu da sanduna bayan da suka daure masa kafafu a wani turken lantarki.
Haka nan kuma mun samu dai cewa wai an zargi dan Najeriyar ne da laifin yin sata a kasar.
Yan Najeriya dai na fuskantar matsi da ma tsangwama a wasu kasashen duniya irin su kasar Afrika ta kudu.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng