An kama mata 8 da ake zargin su da laifin karuwanci a Kano

An kama mata 8 da ake zargin su da laifin karuwanci a Kano

- Jami'an Hisbah sun kama wasu mata da laifin karuwanci a Kano

- Matan sun kasance masu kimanin shekaru 22 zuwa 23

- Mataimakin shugaban Hisba ya ce zai a gurfanar da su a gaban kotu

Jam’ian Hisba na Kano sun kama mata 8 a ranar Alhamis da ake zargin su da laifin Karuwanci, wanda ya saba dokar shariar musulunci a jihar.

Mataimakin kwamdar Hukumr, Malam Nasiru, yace an kama masu laifin ne a tashar mota na Rijiyan Zaki.

An kama mata 8 da ake zargin su da laifin karuwanci a Kano
An kama mata 8 da ake zargin su da laifin karuwanci a Kano

Nasiru ya ce “Jami’an su sun isa wajen da misalin karfe 5pm na yammacin Alhamis kafin suka kama masu laifin a tashar Rijiyan zaki.”

KU KARANTA : Wani mutum ya yi wa diyar matar sa mai shekaru 13 ciki

“Duka masu laifin yara mata ne masu kimanin shekaru 22 zuwa 23.”

Nasiru ya ce an fara kame ne bayan hukumar ta samu rahoton sintirin da yan mata suke yi a tashar. Za a gurfanar da so a kotu dan kamala bicike inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: