Mutum ba a bakin komai ba: wata Amarya ta mutu yayin da take karrama baƙinta
Wata Amarya mai suna Zainad Sodangi ta riga mu gidan gaskiya satuka kadan bayan ta tare a gidan mijinta, mai kaunarta Salim Sodangi, kamar yadda shafin YabaLeft ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa a ranar 29 ga watan Agusta ne aka daura auren Zainab da Angonta Salim, sai dai ta gamu da ajalinta kwanaki 10 da tarewarta a gidan mijin nata.
KU KARANTA: Hatsari ba sai a mota ba: Mutane 56 sun gamu da ajalinsu a hatsarin Kwalekwale
A ranar da ajalin Zainab zai cika, tayi baki da dama yan uwansu da suka kawo mata ziyara da bangajiya, inda ita kuma ta dage wajen karrama su tare da kawo musu kayan kwalam da makulashe.
Bayan ta kammala basu abinci ne, sai amarya Zainab ta zauna akan kujera, shike nan daga nan sai rai yayi halinsa, idan ya kafe yana kallon sama.
Wani daga cikin yan uwan Amaryar daya bayyana rasuwar ta, ta yace sun kadu matuka a sakamakon rasuwar yar uwar tasu, inda yace amarya Zainab ba tayi ciwo ba ko kadan.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng