Lafiya jari: Abinci 5 da ke lalata hantar dan adam

Lafiya jari: Abinci 5 da ke lalata hantar dan adam

- Hanta dai wata tsokace mai matukar anfani

- Hanta na taimakawa dan adam wajen lalata wasu kwayoyin jini da suka lalace

- Ana samun hanta ne a cikin dan adam

Hanta dai wata aba ce mai matukar anfani a cikin jikin dan adam ake samu a cikin cikin dan adam. Ko shakka babu hanta mai lafiya kusan dai-dai take da mutum mai lafiya haka zalika hanta marar lafiya ma dai-dai take da mutum marar lafiya.

Legit.ng ta zakulo mana wasu kala-kalar abinci da ke da matukar tasiri wajen lalata hanta kuma ga su a nan mun jero.

1. Abinci mai kitse

Dukkan dange-dangen abinciccika matsu kitse na da matukar hadari da lafiyar hantar dan adam. Abincin da ke da kitse yakan ba hanta wahala sosai kasantuwar ita ce ke kula sarrafa dukkan abunda ke shiga cikin dan adam. Yawan cin kitse kan cutar da ita sosai.

2. Suga

Lafiya jari: Abinci 5 da ke lalata hantar dan adam
Lafiya jari: Abinci 5 da ke lalata hantar dan adam

KU KARANTA: Kalli bidiyon dan sandan Najeriya da yayi mankas da giya

Kadan daga cikin ayyukan hanta shine sarrafa suga zuwa sinadarin kitse kuma kamar yadda muka karanta a sama, yawan hakan ma kansa yana da lahali ga lafiyar hantar.

3. Gishiri

Binchiken masana ya nuna cewa abinci mai gishiri kan yi lahali ga jiki musamman ma dai kasantuwar hanta ita ce ke da alhakin sarrafa sinadarin. Yawan gishiri kan wahalar da hanta ya sanya mata cuta.

4. Giya

Lafiya jari: Abinci 5 da ke lalata hantar dan adam
Lafiya jari: Abinci 5 da ke lalata hantar dan adam

Shan giya ma dai kan taimaka wajen lalata hantar dan adam kasantuwar cewa takan wahalar da hantar wajen sarrafa ta.

5. Abincin makulashe na gwangwani

Kasantuwar yawancin wadannan abinciccikan nan na dauke da gishiri da suga mai tarin yawa, hakan kuma na matukar wahalar da hanta wajen sarrafawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel