Kara-kara-kaka! Yau za'ayi muhimmin zama tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU
Labaran da muke samu a halin yanzu suna nuni ne da cewa yau din nan Talata 29 ga watan Agusta ake sa ran babban ministan kwadago da samar da aikin yi Dakta Cris Ngige zai yi wani muhimmin zama tare da zababbun shugabannin kungiyar nan ta malaman jami'oin kasar nan watau ASUU a Abuja.
Wannan muhimmin zaman tattaunawar dai kamar yadda muka samu rahoto za'a yi shi ne da nufin lalubo hanyar maslaha tsakanin bangarorin biyu da zummar janye aikin nasu domin daliban su koma makaranta.
Legit.ng ta samu labarin cewa kadan daga cikin tawagar gwamnatin tarayyar da za'a yi zaman da su sun hada da ministan Ilimi, ministan kudi, babban sakatare na hukumar kula da jami'oi, babban sakatare na hukumar kula da kudaden albashi da kuma shugabannin gamayyar kungiyar kwadago.
A tun makon da ya gabata ne dai muka ruwaito maku cewa a wannan satin ne ake sa ran gwamnatin tarayya zata yi wannan muhimmin zaman da kungiyar malaman jami'oin domin kawo karshen yajin aikin da suka shiga na sai baba-ta-gani a ranar 17 ga watan Agustan wannan shekarar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng