Karshen duniya: An kama wata malama da ke zina da daliban ta maza a makabarta

Karshen duniya: An kama wata malama da ke zina da daliban ta maza a makabarta

Wata kotu a kasar Amurka ta bayar da umurnin a daure wata malamar makaranta mai suna Charli Parker dake koyarwa a jihar Alabama bisa zargin ta da akeyi da kwanci da wasu maza daliban ta biyu a makabarta.

Alkalin kotun dai ya yanke hukuncin daurin shekaru 3 ne bayan da wadda ake zargin Miss Parker dake da shekaru 31 a duniya da laifin ta amsa laifin tayi.

Karshen duniya: An kama wata malama da ke zina da daliban ta maza a makabarta
Karshen duniya: An kama wata malama da ke zina da daliban ta maza a makabarta

Legit.ng dai ta samu daga majiyar mu cewa tsohuwar malamar Parker wadda a da ta ke koyar da yara kwallon Basketball da kuma motsa jiki a zarge ta ne da yin lalata har sau goma sha daya da daya daga cikin daliban nata a tsakanin shekara ta 2014 zuwa 2016.

Haka ma dai jim kadan bayan an kama matar sai yan sanda suka kama mijin nata shima inda aka makashi kotu ana zargin sa da laifin kwanciya da wata daliba a makarantar.

Daga karshe muna addu'a Allah ya kiyashe mu tabewa don kuwa wannan mummunan laifi da yawa yake. Suma sauran masu yi ko masu ra'ayin yi to Allah ya tsare su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng