Wata Karuwa ta haifi ýar gaba da Fatiha, ta sayar da ita naira dubu 50 ga wani Attajiri

Wata Karuwa ta haifi ýar gaba da Fatiha, ta sayar da ita naira dubu 50 ga wani Attajiri

Wata Karuwa mai shekaru 22, Blessing Udoh ta gurfana gaban kotu bisa zarginta da ake yi da siyar da jaririyarta mai watanni 3 a Duniya kan naira 50,000, inji rahoton kamfanin dillancin labaru,NAN.

Blessing Udoh ta bayyana gaban kotun majistri ne dake garin Ebute Meta jihar Legas, inda alkalin kotun ya yanke hukuncin a garkame mashi ita a ofishin Yansanda.

KU KARANTA: Murnan cika shekaru 76: tarihin Najeriya ba zai cika ba har sai an ambaci sunan IBB – Inji Saraki

Ana tuhumar Blessing ne kan aikata laifin Karuwanci da kuma cinikin jarirai, amma ta kekasa kasa tace Allanbaran bata da laifi a dukkanin laifukan da ake tuhumar ta dasu.

Wata Karuwa ta haifi ýar gaba da Fatiha, ta sayar da ita naira dubu 50 ga wani Attajiri
Uwa da yarta

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dansanda mai kara Kehinde Omisakin yana bayyana ma kotu cewa Blessing ta aikata wannan laifi ne a ranar 30 ga watan Yuni da misalin karfe 6 na yamma a unguwar Abbatoir dake Oko Oba, yankin Abule Egba, na jihar Legas.

Dansan yace matar ta siyar ta jaririyar tata ne ga wata iyalan Philips James mazauna garin Oron jihar Akwa Ibom, inda ya kara da cewa sun sha kamata tana aikin kilaki.

Daga nan sai alkalin kotun Tajudeen Elias ya dage sauraran karar zuwa ranar 23 ga watan Agusta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel