Buhari: BBC sun soki shugaban kasar Najeriya kan jinya a kasar waje
- Hukumar BBC ta soki shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da sauran shugabannin Afrika dake tafiya kasar waje don jinya
- BBC sun bayyana cewa shugabbib kasashen Najeriya, Angola, Zimbabwe, Benin da Algeria na da halaye iri daya
- Buhari ya dauki tsawon sama da watanni hudu a birnin Landan cikin shekarar nan don ganin likita kan wani cuta da ba’a bayyana ba, wanda hakan ya haddasa rudani a kasar
Hukumar British Broadcasting Cooperation (BBC) ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da “rashin imani da tsarin kiwon lafiyar gida”.
A cewar BBC, Buhari ya kasance a cikin jerin shugabannin Afrika biyar da suka tafi jinya a kasar waje akai-akai ba tare da la’akari da abubuwan da ka iya kaiwa ya komo ba.
Sauran shugabannin sun hada da Abdelaziz Bouteflika (Algeria), Robert Mugabe (Zimbabwe), Jose Eduardo dos Santos (Angola) da kuma Patrice Talon (Benin), Vanguard ta rahoto.
Legit.ng ta tattaro cewa an bayyana Buhari a matsayin “Farko cikin sauran” ta fannin daukar dogon lokaci a kasar waje don samun taimakon likita.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Wike ya kai makami gurin taro, yace a shirye yake yayi yaki da yan adawa
A rahoton, BBC ta bayyana cewa Naziru Mikailu, editan ta na Abuja, ya bayyana cewa tsarin kiwon lafiya a kasar Najeriya ya munanta saboda rashin kulawa ta fannin kudi. A farkon wannan shekara, Buhari ya dauki tsawon kwanaki 49 a birnin Landan.
A halin yanzu Buhari ya dauki tsawon sama da watanni hudu a birnin Landan cikin shekarar nan don ganin likita kan wani cuta da ba’a bayyana ba, wanda hakan ya haddasa rudani a kasar.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng