Matan Sojoji sun cika da murna yayin da mazajensu suka dawo daga jihar Borno lafiya (Hotuna)
- Rundunar Sojin Najeriya ta mayar da wasu sojoji gida daga filin daga
- An kwashe Sojojin ne da suka dade suna fafatawa da yan Boko Haram
A kokarinta na tabbatar da an sauya ma Sojojin da suka dade a bakin daga suna yaki da mayakan yan ta’adda wurin aiki, rundunar Soji ta mayar da wasu Sojoji barikinsu dake fatakwal.
Sojojin da suka fito daga bataliya ta 29 sun koma gida ne biyo bayan wani umarni da babban hafsan Sojin kasa, Laftanar Tukur Yusuf Buratai ya bayar da a sada su da iyalinsu, wanda hakan yayi matukar faranta musu rai.
KU KARANTA: Fin ƙarfi: Yadda wani fasinja ya suburbuɗi direba a cikin motarsa kuma ya hana shi kuɗin mota
Sojojin na daga cikin wadanda suka rayu bayan kwashe shekaru da dama suna yaki da yan ta’adda, a jawabinsa, kwamandan runduna ta 6, Manjo janar EO Udoh yayi ma Sojojin maraba da dawowa gida, sa’annan ya jinjina musu.
Legit.ng ta ruwaito kwamandan ya bukaci da su taya abokanan aikinsu da suke bakin fama da addu’a domin samun nasara akan yan Boko haram, sa’annan ya shawarce su dasu dage wajen bada gudunmuwa a duk lokacin da aka kiraye su.
Ga sauran hotunan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Tsohon soja yace kada ayi yaki, kalla:
Asali: Legit.ng