Yayi shigar mata don ya zana ma budurwarsa jarabawa

Yayi shigar mata don ya zana ma budurwarsa jarabawa

- Matashi yayi shigar mata don ya rubuta ma budurwarsa jarabawa

- Matashin ya shiga hannu bayan masu binciken jarabawa suka kama shi

Wani matashi ya shiga hannu bayan an kama shi yana rubuta ma budurwarsa jarabawa, Legit.ng ta ruwaito mai kula da jarabawar ne ya kama wannan matashi.

Wannan saurayi ya badda kama ne ta hanyar daura gashin doki, da kuma yi ma kansa fente fente, duk dan yayi kama da mace, amma duk da haka masu tsaron jarabawar sai da suka kama shi.

KU KARANTA: Saudiya ta baiwa Najeriya kyautan kilo 181,437 na dabino

Nan da nan jami’an tsaro suka kafa masa ankwa, suka yi awon gaba da shi.

Yayi shigar mata don ya zana ma budurwarsa jarabawa
Matashin

Yayi shigar mata don ya zana ma budurwarsa jarabawa
Saurayin

Yayi shigar mata don ya zana ma budurwarsa jarabawa
Saurayin da budurwar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel