Dandalin Kannywood: Fada ya kacame tsakanin Nafisa Abdullahi da Rahma Sadau

Dandalin Kannywood: Fada ya kacame tsakanin Nafisa Abdullahi da Rahma Sadau

- Surutun da Rahama Sadau ta keyi na cewar ‘yan matan hausa film nada girman kai da bakin ciki, tana jin haushi ne kawai saboda an koreta.

- Sananniyar ‘Yar wasan Hausa Film Nafisat Abdullahi ta mayar da martani akan kalaman da korarriyar jarumar nan Rahama Sadau tayi akan ‘yan Matan Hausa Film, inda ta zarge su da hassada da girman Kai.

Nafisa Abdullahi ta bayyana cewar, kalaman da Rahama Sadau ta keyi sambatu ne kawai na jin haushin korar da akayi mata a Masana’antar film, amma duk da haka ya kamata Rahamar ta sani cewar Matan Hausa Film sun wuce da tunanin ta, saboda Mata ne wayayyu masu ilimi wadanda suka fahimci rayuwa.

Dandalin Kannywood: Fada ya kacame tsakanin Nafisa Abdullahi da Rahma Sadau
Dandalin Kannywood: Fada ya kacame tsakanin Nafisa Abdullahi da Rahma Sadau

Legit.ng ta samu labarin cewa indai jama’a basu mance ba, a wata tattaunawa da akayi da Rahama Sadau ta soki lamirin ‘Yan Matan Hausa Film, inda ta bayyana su a matsayin masu hassada da kyashi gami da girman kai, sannan tayi kira ga shugabannin Kungiyar ta Kanneywood dasu mike wajen magance matsalar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel