Ana neman taimako ‘yan Najeriya fisabilillah
- Ana neman taimakon al’umma domin ceto wannan bawan Allah daga masalar rashin lafiyar da yake fama da
- Wannan mutumin dai na fama da matsanaicin ciwon kansa na saifa
- Ana bukata akalla kudin naira miliyan 3 don masa aiki da sayen magani
'Yan uwa ana neman a taimaka wa wannan bawan Allah domin ceto rayuwarsa.
Sunan sa Malam Muhammad Kasim dake gidan kanawa (Unguwar Kanawa) Kontagora Jihar Neja, yana fama da matsanaicin ciwon kansa na saifa, ankaishi asibitin Kwararru na Bida (Federal Medical Center Bida) inda likitoci suka aunashi suka tabbatar da ciwonsa yayi tsanani, yana bukatar ayi masa aikin gaggawa domin ceto rayuwarsa,
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, kudin da ake bukata don masa aiki da sayen magani naira miliyan 3 gashi da iyali abunda ma zaici sai an taimaka masa.
Da wannan yake rokon gwamnati, da attajirai, da 'yan uwa da a taimakeshi domin ceto rayuwarsa alfarmar wannan wata na azumi mai falala da daraja.
KU KARANTA: Aiki sai mai shi: Gwamnatin jihar nan ta Arewa zata samar da guraben aiyuka 2000 ga matasa
Ga mai sha'awar taimaka masa ga account Number sa:
Suna: Muhammad Kasim
Banki:UBA Bank
Lambar Banki: 2010293197
Domin karin bayani za'a iya tuntubar lambar wayar dan uwansa dake jinyarsa : 08066551335
Allah yabada ikon taimakawa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga bidiyon inda sunan Allah ya bayyana a jikin itacen moringa
Asali: Legit.ng