Kyamar musulunci ta'addanci ne - Shugaban majalisar dinkin duniya

Kyamar musulunci ta'addanci ne - Shugaban majalisar dinkin duniya

- Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, ya ce, nuna kyama ga addinin Islama na rura wutar ta’addanci a sassan duniya.

- Guterres ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da sarki Salman na Saudiya da kuma ministan cikin gidan kasar Mohammed bin Nayef a birnin Riyadh, a karshen mako.

Kalaman babban magatakardar na majalisar dinkin duniya Antonio Gutteres, na zuwa a dai dai lokacin da wasu kasashe ke ci gaba da nuna kyamar karbar baki, musamman wadanda suka fito daga kasashen Musulmi.

Babban magatakardar ya ce, nuna kyama ga Islama, wani goyon bayan ne da kungiyar ISIS ko kuma Da’esh ke samu don cigaba da yada Farfagantarta.

Legit.ng ta samu labarin cewa kungiyar ta ISIS dai ta dauki allhakin kaddamar da munanan hare-haren ta’addanci a Saudiya da kuma nahiyar Turai.

Kyamar musulunci ta'addanci ne - Shugaban majalisar dinkin duniya
Kyamar musulunci ta'addanci ne - Shugaban majalisar dinkin duniya

‘Yan siyasar turai da ke kyamar baki, kamar su Marine Le Pen ta Faransa, sun kara samun karbuwa bayan samun matsalar kwararar bakin haure a nahiyar, wadanda akasarinsu sun kauracewa yake-yake ne daga kasashensu na asali kamar Syria da Iraqi.

Mr. Gutetres ya ce, babu yadda za su samu nasara kan yaki da ta’addanci a Syria ba, matukar ba a samar da mafitar siyasa ba ga al’ummar kasar.

Gutteres dai ya isa Saudiya ne daga Turkiya, kuma ana saran isarsa Dubai a yau Litinin don halartar taron gwamnatocin kasashen duniya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng