Ashe ana gab da samar da rigakafin cutar kanjamau

Ashe ana gab da samar da rigakafin cutar kanjamau

- Shugaban hukumar NACA Sani Aliyu ya ce kasa Najeriya na kokarin ganin ta dakile yaduwar cutar kanjamau ta hanyar tabbatar da cewa mutane da ke dauke da cutar sun sami ingantaciyar kular da suke bukata.

- Sani ya fadi haka ne a taron wayar da kai da akayi a Abuja.

Sani Aliyu ya ce samar da alluran rigakafin cutar kanjamau na da mahimmanci domin hakan zai taimaka wajen rage yaduwar cutar musamman ga jarirai da ke kama cutar tun suna cikin uwayensu.

Legit.ng ta samu labarin cewa Bayan haka shugaban cibiyar bincike ta kasa da kasa kan cututtuka Alashle Abimiku ta tabbatar da cewa sashen binciken ta fitar da kyawawan sakamako akan kokarin da ake yi na samar da alluran rigakafin cutar kanjamau.

Ashe ana gab da samar da rigakafin cutar kanjamau
Ashe ana gab da samar da rigakafin cutar kanjamau

KU KARANTA: Gobara tayi ta'asa a wata kasuwa a Arewa

Alashle Abimiku ta kasashen duniya da yawa suna kokarin samar da allurar rigakafin cutar domin ganin a dakile yaduwar cutar.

Kasa Najeriya ce ta biyu da ta fi yawan mutanen da ke dauke da cutar kanjamau a duniya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: