Gidan labarin BBC ta nemi gafarar Sarkin Kano kan labarin da ta rubuta a kansa
- Abinda muka rubuta cewa za’a binci Sarkin Kano lallai ba hakan ba daidai bane kuma muna rokon sa daya yi hakuri, inji Jamie Angus
- BBC ta nuna cewa kuskuren ya aukune daga kuskuren fassarar hirar da tayi da da shugaban hukumar da ke binciken yadda aka kashe kudaden masarautar Kano
Labarin da kafar yada labaran ta BBC tayi rokon afuwar kuskuren nata akai shine badakalar kudaden masauratar Kano da aka zargi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II Sanusi kashe su ba akan ka’ida ba.
BBC ta nuna cewa kuskuren ya aukune daga rashin daidan wanda ya fassara hirar da tayi da da shugaban hukumar da ke binciken yadda aka kashe kudaden masarautar Mahyi, Magaji ne bai yi dai-dai ba, inda kuma su a can kasar Britaniya suka wallafa shi a zaman dai-dai ne.
Jamie Angus, Babban Daraktan Editocin BBC ne ya sanar da hakan a wasikar da BBC din ta rubuta wa Sarki Sanusi, inda ya ce BBC ya rubuta wa sarkin wasika ta musamman ne domin neman ya yi hakuri akan kuskuren da su kayi.
KU KARANTA: Sarki Muhammadu Sunusi ya biya naira miliyan 6 don yi wa mara lafiya aiki
“Bayan an gudanar da hirar, an mika ma wani abokin aikin mu ne a ofishin mu dake Abuja domin ya fassara kafin aka aiko dashi Landan”
A Nakaltowar Legit.ng daga Angus; yace:: "Gudanar da bincike akai ne yasa muka gano cewa abinda muka rubuta ba daidai bane da abinda shi Muhyi ya fadi a hirar tasa in da shi da kansa ya sanar mana cewa ba’a gaiyace ka ba a zaman kwamitin dake binciken wannan badakala."
“Abinda muka rubuta cewa wai kaima za’a bincikeka lallai ba haka bane kuma muna rokon ka da ka yi hakuri.” Jamie Angus
Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/
Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng