Karshen duniya! Wata yarinya ta kashe kanta saboda son da take yiwa malamin ta

Karshen duniya! Wata yarinya ta kashe kanta saboda son da take yiwa malamin ta

- Masu hikimar magana na cewa, in da ranka za ka ga abu da yawa

- Wannan tabbas haka yake, bisa la'akari da abubuwan ban al'ajabi da takaici da ke faruwa yau da kullum, wanda kan sa mutum ya fara kokwanto, anya ba almara ba ce?

Wani al'amari mai sanyaya zuciya, ya faru a kauyen Mista Ali a karamar hukumar Bassa da ke jihar Filato, inda wata yarinya matashiya mai kimanin shekaru 13, mai suna Basma Ali ta sha maganin bera ta kashe kanta, saboda wani abin kunya da ya faru tsakanin ta da wani malamin su, wanda take jarabar so.

Legit.ng ta tattaro cewa Basma dai ta shaidawa wata kawarta irin halin da take ciki na son malamin nasu, wanda aka boye sunan sa, inda ita kuma ta ba ta shawarar ta rubuta masa wasika. Hakan kuwa aka yi. Basma ta rubuta masa tare da bayyana masa cewa zuciyar ta na kaunar sa, kuma tana neman ya amince mata.

Tun da ta bashi wasikar malamin nasu bai ce mata komai ba, har tsawon wani lokaci, abin da ya sa hankalin Basma ya tashi. Don haka ta rubuta masa wata wasikar, inda ta sake bayyana masa halin da take ciki da kuma bukatar ta na ya yi amfani da ita!

Karshen duniya! Wata yarinya
Karshen duniya! Wata yarinya

Wannan wasika ta biyu da bukatar da yarinyar ta gabatar ya yi matukar bata ran malamin, wanda bai yi wata wata ba ya garzaya zuwa wajen shugaban makarantar tare da nuna masa wasikar da yarinyar ta aika masa.

Ba tare da bata lokaci ba, shugaban makaranta ya tara sauran malamai aka kira taron dalibai gaba daya tare kuma da kiran Basma gaban sauran dalibai aka ba ta wasikar da ta rubuta a kan ta karanta kowa ya ji. Amma saboda tsoro da kunya ba ta iya karantawa ba, sai malamin ne ya karanta kowa ya ji abin da wasikar ta kunsa.

KU KARANTA: Ku kalli wanda Shugaba Buhari ya nada a hukumar hada motoci

Sakamakon laifin da yarinya Basma ta yi, shugaban makarantar ya sa an yi mata bulala 15 a gaban dalibai, sannan aka kora ta gida, tare da bukatar washegari ta je da babanta.

Hukuncin da ta fuskanta a gaban dalibai da tona mata asirin da malamin su ya yi, sun sa Basma ta yi kwanan bakin ciki da damuwa, don ba ta san yadda za ta tunkari mahaifinta da zancen ba. Don haka ta aika wani kanin ta ya je ya sayo mata maganin bera ta sha ta ce ga garin ku nan.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ko me zai sanya ku kashe kanku? Legit.ng ta tambayi wasu yan Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng