Hadarin kwale-kwale ya hallaka mutane 7, guda 7 na asbiti kuma 133 sun bace
- Akalla mutane 7 ne suka rasa rayukansu, 7 sun jikkata, kuma saura ba’a san inda suke ba
- Hadarin ya farune ranan Juma’a yayinda kwale-kwalen ke hanyar dawowa daga kasuwan Malali sai taci karo da bishiya
Akalla mutane 7 ne suka rasa rayukansu, 7 sun jikkata, kuma saura ba’a san inda suke ba a karamar hukumar Ngaski na jihar Kebbi inda wata kwale-kwale dauke da mutane 150 ta kife cikin tekun Neja.
Shugaban hukumar kawo agaji na gaggawa wato NEMA na jihar Sokoto, Kebbi, da Zamfara, Alhaji Sulaiman Muhammad, ya tabbatar da faruwan wannan hadari a yau,asabar ga jaridar NAN.
Yace masunta da jami’an hukumar ruwan Najeriya na iyakan kokarinsu wajen nemo wadanda suka bace.
“Lokacin da muka samu labarin abinda ya faru, muka kira hukumar ruwa ta taimaka wajen ceto wadanda suka bace.
KU KARANTA: Bani da matsala da Dogara, kani na ne - El- Rufai
“Dukkan mutanen da ke cikin kwale-kwalen ne suka bace, yayinda ake bincike, an gano 14; 7 sun mutu, 7 sun jikkata kuma suna asibitin Ngaski.”
Legit.ng ta tattaro cewa hadarin ya faru ne yayinda kwale-kwalen taci karo da wata bishiya da ke cikin tekun, sai ta kife.
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng