Yarona ya fara kisan kai tun yana shekara 12 – Mahaifiyar dan fashi
Mahaifiyar wannan babban dan fashin da aka kashe, Henry Onyekachi Chibueze, wanda ya fi shahara da suna Vampire. Tace shaidanin yaro ne kuma da ma ya addabe su a dangi.
Mrs Beatrice Chibueze ta fadawa jaridar Sun cewa yaronta ya fara kisan kai tun yana dan shekara 12 a makarantan firamaren Umuokpu Community, lokacin yana aji 4.
Legit.ng tana tuna muku cewa Vampire ta rasa ransa a a ranan 2 ga watan Maris, a dajin Umuuowa a karamar hukumar Ikwerre a jihar Ribas yayinda wata rundunana yan sanda ta musamman ta je farautarsa.
KU KARANTA: Daliba ta kashe kanta a makaranta
Tace: “An haifi Henry Onyekachi Chibueze a shekarar 1981. Marigayi mijina ta sa shi a makarntan firamare a Umuokpu a Abaja, amma ya fita daga makaranta a aji 5 bayan ya kashe wani abokin sa yayinda suke fada yana dan shekara 12.
“Wannan abu ya tayar da hankali a dangin mu har sai da mahaifinsa ya biya diyya. Henry ya kasance yana halayya Kaman wanda aka tsinewa.
“Lokacin da ya bar makarantan firamare, yaki koyan wani aikin hannu, kawai sai ya fara bin yan iskan unguwa inda ya fara fashi da garkuwa da mutane.”
https://twitter.com/naijcomhausa
https://web.facebook.com/naijcomhausa/#
Asali: Legit.ng