An gano babban sirrin Buhari da yayi anfani dashi wajen murkushe Boko Haram
- Babban Hafsan Dakarun Tsaron Najeriya ya ce kasar ta kashe fiye da dala biliyan biyu da miliyan dari shida a shekarar 2016 kawai domin bayar da agaji ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa
- Janar Abayomi Olonisakin ya bayyana haka ne a wurin wani taro da aka yi a birnin Washington na Amurka a kan gamayyar da ake yi wajen murkushe kungiyar IS
A cewarsa, "Duk da kashe fiye da dala biliyan biyu da miliyan dari shida da gwamnatin Najeriya ta yi a 2016 domin bayar da agaji ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa, har yanzu akwai bukatar bayar da tallafi, musamman bayan an sake kwato garuruwan da ke hannun 'yan kungiyar."
KU KARANTA: Dole in gaya wa Buhari gaskiya ko da za'a sauke ni daga sarauta ta
"Yawancinku da ke wannan dakin sun zo taron da muka yi a Oslo babban birnin kasar Norway a watan Fabrairu domin nuna goyon bayansu ga Najeriya. Hadin gwiwa na da matukar muhimmanci. Don haka muna gode wa Sakatare Rex Tillerson da Shugaba Donald Trump saboda jajircewarsu ta yaki da makiyin duniya - ta'addanci."
Ya kara da cewa yakin da kasar Iraki ke yi da kungiyar IS irinsa Najeriya ke yi da Boko Haram.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng