Yadda wata Akuya tayi sanadiyyar mutuwar mutane 5
Wani labari daya watsu a kafar sadarwa ta Facebook kan yadda wata Akuya ta yi sanadiyyar mutuwar mutane shidda sakamakon wani mummunar hatsarin data janyo.
Wani ma’abocin kafar sadarwa ta Facebook D’Young C Ben Collins ne ya bada labarin yadda Akuyar ta janyo faruwar wata mummunar hatsarin data lakume rayukan mutane shidda a jihar Anambra yayin da matafiyan ke dawowa daga garin Oko.
KU KARANTA: Toh fa! Rikici ta kunno kai a majalisar wakilai kan lafiyar shugaba Buhari
Sai dai abin mamakin shine, Akuyar bata ji kwarzane ba, duk da cewa ita ma ta rigu mu gidan gaskiya.
Ga dai yadda Collins ya bada labarin:
“Kai, wani hatsarin ban mamaki ya faru, inda Yariman garin mu yayi hatsari tare da daliban kwalejin kimiyya dake Oko, a lokacin dayake kan hanyarsa ta dawowa daga Oko, inda mutane shidda suka rasu, ciki har da dalibai 5 da direban motar.
“Dayake akuyar bata ji ciwo ba, amam dai ta mutu, sai mutane suka yanka ta don yin banda, amma duk da yankan ba’a samu jini a jikinta ba. A yanzu haka yariman garin mu na asibiti inda ya smau karaya a hannaye da kafafuwa. Mutum daya ne kawai ya fita ba tare da jin ciwo ba”
Ga hotunan nan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng