Sojojin Najeriya sun nuna wa duniya makaman da suka kera (Hotuna)

Sojojin Najeriya sun nuna wa duniya makaman da suka kera (Hotuna)

Rundunar Sojin Nijeriya ta shirya taron bajen kolin kayayyakin yaki na kwanaki uku a Abuja, inda ta gabatar da motoci da bindigogin kai farmaki daban-daban.

Sojojin Najeriya sun nuna wa duniya makaman da suka kera (Hotuna)
Sojojin Najeriya sun nuna wa duniya makaman da suka kera (Hotuna)

Taron wanda aka fara gabatarwa a yau Litinin a Babban Dakin Taro na “Nigerian Army Resource Centre” dake Barikin Mambila a Abuja a karkashin jagorancin Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Tukur Yusuf Buratai ya samu halartar Ministan Tsaro, Janar MA Dan’Ali da Ministan Kimiyya da Fasaha, Dakta Ogbonnaya Onu.

KU KARANTA: Sako daga fadar shugaban kasa

Ministan Tsaron, wanda ya jagoranci manyan baki a yayin zagayen kaddamar da kayakin yakin, ya bayyana cewa wannan yunkuri shine irinsa na farko da Nijeriya ta fara kera kayakin yaki na kanta.

“Hakika wannan babbar nasara ce da Nijeriya ta cimma a karkashin jagorancin Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari don tabbatar da zaman lafiya a kasar nan.”

Haka Zalika shima Babban Hafsan Sojin, Tukur Buratai ya ce wannan duka yana daga cikin yunkurin kawo karshen ta’addanci a Nijeriya….

“Muna tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa kowa ya kwantar da hankalinsa da yardar Allah zamu kawo karshen kowane ta’addanci a kasar, kamar yadda ake gani mun riga mun gama da Boko Haram illa kawai kananan hare-hare da ake samu nan da can.”

Babban Bako mai jawabi, Tsohon Darakta Janar na Hukumar Kimiyya da Fahasa kuma Sakataren Gwamnatin Jihar Adamawa, Fasfesa Buba Bindir ya bayyana irinmuhimmancin dake tattare da Kimiyya da Fasaha wanda ya kai ga samun nasarar samar da wadannan dabaru, “babu wata kasa a duniya da ta taka tsanin cigaba a duniya face sai da ta samu nasara a fannin Kimiyya da Fasaha. Don haka mu ma a Nijeriya mun kama hanyar wannan nasara muddin muka cigaba da dogaro da kanmu.” In ji shi.

Kayakin yakin da rundunar sojin ta gabatar sun hada da tankokin yaki biyu, motocin yaki masu sarrafa kansu guda 10, motocin kai farmaki 10, mashunan yaki 20, bindigogi da alburusai da sauran su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng