Yayi lalata da diyar cikin sa, sai matar sa tayi mashi wannan mummunan hukuncin (Karanta)
- A ranar Talatan nan ne dai wata matan aure mai suna Blessing Ilo ta maka mijinta a wata kotu dake garin Abuja saboda tuhumarsa da takeyi akan aikata zina da’yar cikinsa da take zama tare dasu
- Blessing ta fada wa kotu cewa mijinta na lalata da yarinyar ne wanda ‘yar shekara 12 ne kacal a duk lokacin da ta fita zuwa wajen aiki
Ko da yake ba itace mahaifiyar yarinyar ba mijin nata ya gaya mata cewa tsohuwar matarsa ce ta haifeta.
‘Yarinyar ta taba sanar da ‘yan sanda cewa mahaifin nata na daure mata hannaye kafin ya yi lalata da ita tun a baya.
Blessing ta sanar wa kotu cewa dole ta tattara inata-inata ta bar gidan domin mijin ta mashayin giya ne na gaske.
Tace idan ya sha giyarsa ya bugu yakan yi mata fitsari a gadonsu na kwanciya, ko kuma a tsakar daki ko cikin randar ruwan da suke sha. Sannan baya ciyar da ita da dan da ta haifa masa sannan baya biyan kudin makarantar dan.
Blessing ta roki kotun da ta raba aurenta da shi mijin nata kuma ta bata ikon rike dan da suka haifa.
Alkalin kotun Jemilu Jega ya ce kotu ta kai wa mijin Blessing sammace har sau uku amma ya ki zuwa kotu don haka ya daga shari’ar karan zuwa 9 ga watan Faburairun 2017.
Asali: Legit.ng