Bincike: Sojoji na yi wa yan gudun hijira ciki sannan kuma su gudu a Borno

Bincike: Sojoji na yi wa yan gudun hijira ciki sannan kuma su gudu a Borno

- ‘Yan mata da dama ne Sojojin Najeriya suka yi amfani da su kuma kafin matan su gano suna dauke da juna biyu an dauke Sojojin daga Jihar Borno mai fama da rikicin Boko Haram.

- Wasu matan da Kamfanin dillacin labaran Faransa AFP ya zanta da su a Maiduguri sun ce sojojin sun jefa rayuwarsu cikin kunci.

Bincike: Sojoji na yi wa yan gudun hijira ciki sannan kuma su gudu a Borno
Bincike: Sojoji na yi wa yan gudun hijira ciki sannan kuma su gudu a Borno

Ummi Hassan ‘yar shekaru 18 ta ce tana dauke da ciki watanni biyu aka dauke sojan da ya mata cikin zuwa Lagos kuma ya barta cikin wahala duk da suna magana a waya.

Ummi ta ce abincin da ma za ta ci yana ma ta wahala.

Akwai Kaltime Ari da Amina Muhammed da sojoji suka yi wa ciki kuma har suka haihu ba su yi ido da iyayen ‘ya’yan ba.

Yanzu Matan sun ce sun koma yin bara domin samun na abinci da hidima da ‘yayansu saboda halin kuncin rayuwa da suka tsinci kansu a ciki.

A bara, Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun zargi sojoji da ‘Yan sanda da ‘Yan kato da gora da yi wa mata fyade a sansanonin 'Yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.

Kungiyar Human Rights Watch ta ce akwai irin wadannan matsalolin kusan 43 da ta tattara inda jami’an tsaro ke tilastawa mata yin jima’I da su ta hanyar alkawarin za su aure su ko ba su abinci da kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng