Shin ko namijin goro na da amfani ga lafiya?

Shin ko namijin goro na da amfani ga lafiya?

Namijin goro wanda a ka fi sani da 'garcinia kola' yawanci a fi samunsa a kasashen Afirka, kuma shekaru aru-aru a na amfani da shi don yin magani a al'adun Afirka, don sai ku gyara zama ku karanta fa’idar amfani da shi ga lafiyar ka.

Shin ko namijin goro na da amfani ga lafiya?
Shin ko namijin goro na da amfani ga lafiya?

Ya na dauke da sinadarin 'dimeric flavonoid' wanda a ke ganin ya na yin magunguna da dama. A yau za mu fada muku manya-manyan amfanin namijin goro.

A na noman wannan dan itace ne a kasashen Najeriya, da Kamaru, da Ghana, da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, da Benin, da Kwadebuwa, da Gabon, da Saliyo, da Laberiya, da kuma Sanegal. Mutanen Afirka sun dade da gano amfanin namijin goro ga lafiya.

A tarihance, likitoci a Afirka sun yi imani cewa, namijin goro na da sinadarin yakar kaska, da yashe ciki, da kuma yakar kananan kwayoyin cuta. Da farko dai likitoci na amfani da shi don maganin tari da cututtukan makogwaro, da bututun iska, da ciwon kai ko sanyin kirji, da kuma ciwon ciki.

Bugu da kari, tsarin maganin gargajiya na Afirka ya nuna masu matsalar hanta ka iya tauna namijin goro.

Wannan dan itace na taimaka wa wajen maganin dukkan nau'i na tari, a na kuma amfani da shi wajen maganin sanyi.Yawanci kuma ya fi amfani wajen kakkabe mashako, da tari, da toshewar hanci, da kuma majina.

Namijin goro ya na taimakawa wajen yakar miyagun cututtuka kamar Ebola, ya na kuam dauke da sinadaran yakar dadewar fata da sauransu. Ya na kara karfin kwaranyar jini ga mutanen da ke da matsala da bututun da ke dauko jini daga zuciya.

Sannan ya na taimaka wa garkuwar jiki,domin binciken kimayya na musamman ya tabbatar da cewa, yawan amfani da shi na ba da kariya ga garkuwar jikin dan adam.

Har ila yau Namijin goro na warkar da ciwon gwiwa wajen rage mata radadi sosai yana kuma amfani wajen jin yunwa sannan ya na sa jin kishirwa.

Kammalawa

Mutanen Afirka sun dade da gano amfanin Namijin goro. Su na amfani da shi don dalilai da yawa. Tsarin magungunan gargajiya na Afirka na amfani da namijin goro don maganin cututtuka masu yawa. Duk da haka ya kamata mutane su tuntubi likita kafin amfani da namijin goro don kare lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng