Ƙarya ne, ni ba Yesu bane, inji wani Bature

Ƙarya ne, ni ba Yesu bane, inji wani Bature

Wani bakon mutum, bature dan asalin kasar Australia daya bayyana a kasar Kenya da mutane suke kiransa da Yesu Almasihu (A.S) ya musanta zancen mutanen.

Ƙarya ne, ni ba Yesu bane, inji wani Bature

Hakan dai ya faru ne tun bayan da Baturen ya isa kasar Kenya inda ya shiga kasuwa don yin siyayya, amma sai mutanen kasar suka ga yayi musu kama da mutumin nan daya kwaikwayi Yesu a wani wasan kwaikwayo da aka taba yi, nan da nan jama’a suka taru suna daukan hoto da shi suna kiran ‘Yesu ya dawo’, yayin da wasu kuma suka shirya masa walima suna gayyatan shi gidajen su.

Ƙarya ne, ni ba Yesu bane, inji wani Bature

Sai dai wannan mutumin mai suna Daniel Christos dan asalin kasar Australia ya karyata batun cewa shine Yesu, Christos yace shi ba mabaraci bane, asali ma shi yazo yawon bude ido ne daga garin Perth na Australia. Christos ya mayar da martanin ne a shafinsa na Facebook bayan wani ma’abocin kafar sadarwar ta Facebook Mook Carter III yayi barazanar zasu kafa kwamiti don su gicceye shi tare da wasu barayi biyu.

Ƙarya ne, ni ba Yesu bane, inji wani Bature

KU KARANTA: Wasu Yan Amurka sun bukaci musulmai su bai kasar

Christos yace ganin yadda jama’a suka fara yi ma rayuwarsa barazana ya sanya dole yayi ma jama’a bayani.

Inda yace: “Kimanin sati biyu kenan nazo yawon bude ido daga kasar Ethiopia, kuma na samu karbuwa sosai daga mutane fiye da yadda nake tunani. Saboda duk inda na shiga a garin Nairobi, sai kaga wasu mutane na daukana hoto, wasu kuma na daukan bidiyo inda zaka ji suna kirana ‘Yesu’!

Ƙarya ne, ni ba Yesu bane, inji wani Bature

“A gaskiya jama’an kasar Kenya sun nuna min karamci, amma daga lokacin da naga maganan wasu mutane da suka ce zasu gicciye ni sai na shiga damuwa, naga ya kamata nayi karin haske ga mutane, ban sani ba ko da wasa suke koda gaske, amma dai wannan barazana ne ga rayuwa ta, don haka ba zan iya fita gari ba. Don haka ne nake bayyana ma mutane cewa NI BA YESU BANE, KUMA BAN TABA IKIRARIN ZAMA SHI BA.

“Ni matafiyi ne daya kawo ziyara bude ido kasar nan, ina fatan nan gaba idan Yesu ya dawo yazo kasar ku, zaku girmama shi fiye da yadda kukayi min, nagode.”

To ya kuke ganin wannan?

Za iya samun labaran mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng