An kashe mutane 3 a rikicin garin Suleja

An kashe mutane 3 a rikicin garin Suleja

Hukumar yansandan jihar Neja ta tabbatar da mutuwar mutane Uku a wata hatsaniya data kaure a garin Suleja a ranar Litinin 21 ga watan Nuwamba.

An kashe mutane 3 a rikicin garin Suleja
Babban hafsan Yansada Ibrahim Idris

Kaakakin hukumar Ýansanda ASP Bala Elkanah ya bayyana ma kanfanin dillancin labarai a yau Talata 22 ga watan Nuwamba a garin Minna, sai dai yace jami’ansu sun tabbatar da zaman lafiya a garin.

Elkanah ya bayyana abin daya sabbab rikicin, inda yace “wani barawo daya sace wayar wani mutum, sai ya caka ma mutumin wuka yayin da yake kokarin binsa da gudu. Nan da nan jama’a suka bi shi suka kama shi, inda suma suka caka masa wuka. Daga bisani sai yansanda dake sintiri suka iso wurin, inda suka garzaya da mutane uku da suka jikkata zuwa asibiti, sai dai da isan su Asibiti suka ce ga garinku.

KU KARANTA: Saniya ta kade mota a Abia

“Amma yanzu mun dawo da zaman lafiya, don haka muna bukatar jama’a da su cigaba da gudanar da ayyukansu day au da kullum ba tare da karya doka ba, mu kuma zamu cigaba da gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata laifin,” inji Elkanah.

Wani shedar gani da ido ya bayyana ma NAN cewar yansanda sun karkatar da ababen hawa dake kan hanyar shataletalen Sarki da Ofishin yansanda na B. hakan ya sanya matafiya masu zuwa Abuja canza hanyar da zata fitar dasu.

A wani labarin kuma, kimanin wata guda daya gabata kenan wutan lantarki ya lahanta wata mata mai suna Zuwaira Musa a garin Suleja bayan ta kama wayar wuta yayin da take shanya kayan wanki, hakan ya sanya wutar nanata da kasa.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel