Kaso uku cikin dari na matan Adamawa na mutuwa
- Mata masu juna biyu dubu tamanin ake saran zasu anfana daga agajin kayan haihuwa a kananan hukumomi ashirin da daya dake jihar Adamawa.
- Shugaban kungiyar kyautata jin dadin rayawa da koyar da sana’o’i don dogaro da kai mai zaman kanta Alhaji Ahmed Lawal ya bayyana haka da yake kaddamar da shirin a Fufore inda matan karkara masu juna biyu kimanin dubu takwas suka anfana da kayan haihuwa kyauta.
Rabon agajin kayan haihuwan inji shugaban kungiyar ya biyo bayan bayanai na cibiyar kula da kiwon lafiya matakin farko ke nuna a kalla mata uku daga cikin dari ke mutuwa lokacin haihuwa ko kasa da sa’o’I ashirin da hudu bayan sun sauka saboda dalilai na jahilci da talauci. Yana mai nuni da akwai mata da ke asarar ransu saboda basu da sukunin sayan reza idan nakuda ta taso.
KU KARANTA: Tsagerun Neja Delta sun fasa bututun mai
Yayin da shi kuma shugaban cibiyar kula da kiwon lafiya matakin farko na jihar Adamawa Dr, Abdullahi Belel ya ce matsalar da ke yawan jawo mutuwar mata lokacin haihuwa shine na rashin tsabtar muhallin da matan kan haihu musamman a yankunan karkara inda ake anfani da ngwarzoma wajen karbar haihuwa.
Matsalar ta fi kamari a kananan hukumomi bakwai na arewacin jiha da rikicin Boko Haram ya tozarta rufe cibyoyin karbar haihuwa dalili ma ken an inji likita da ya sa yankunan komawa ga anfani da ngwarzoma.
Wasu mata masu juna biyu da suka anfana daga agajin kayan haihuwa Malama Lami Mohammed da Malama Maryam Abubakar sun ce dalilin wannan gudumawar zasu soma zuwa awo tare da fatan idan lokacin saukarsu ya yi zasu je asibiti mafi kusa.
A wani labarin kuma, A Najeriya wasu har sun fara kada gangar siyasar 2019, yayin da wasu ke ganin lokaci bai yi ba tukunna.
Tun daga yanzu wasu magoya bayan tsohon Shugaban Najeriya kuma jigo a jam'iyyar APC, Atiku Abubakar (Turakin Adamawa) sun fara tuna ma 'yan Najeriya cewa za su so gwaninsu ya yi takara a shekara ta 2019.
An mai da bukin kaddamar da wata hanya a jahar Adamawa wata dama ta rada ma 'yan Najeriya cewa Turaki fa na nan tafe a 2016. Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Jahar Adamawa Alhaji Abdurrahman Abba Jimeta, ya ce lokaci ya wuce da mai kaza zai ci kai. Ya kara da cewa naka sai naka, Don haka su 'yan Adamawa za su taka rawar gida.
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng