Ana jimamin mutuwar Kanar Abu Ali

Ana jimamin mutuwar Kanar Abu Ali

- A yau Litinin ne hukumomin sojin Najeriya ke jana'izar kwamandan rundunar sojin kasar ta 272 mai kula da tankokin yaki, Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, tare da wasu sojoji hudu

- Kwamandan da sauran sojojin hudu sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke kokarin dakile wani harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai kan barikin sojin kasar na 119 da ke garin Malam Fatori a jihar Borno

Ana jimamin mutuwar Kanar Abu Ali
Ana jimamin mutuwar Kanar Abu Ali
Late Lt. Col Mohammed Abu Ali
Ana jimamin mutuwar Kanar Abu Ali

Haka ma wasu sojojin hudu sun samu raunukka yayin da mayakan Boko Haram 14 suka halaka a cikin artabun na yammacin ranar Asabar.

A shekara ta 2015 ne Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi wa Muhammad Abu-Ali karin girma daga Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai shekarun samun karin girman, saboda jaruntar da ya nuna da ta kai ga kwato yankuna da dama daga hannun mayakan na Boko Haram.

Karshen satin da ya gabata ne dai Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, tare da wasu sojojin hudu, lokacin da suka dakile wani harin mayakan Boko Haram a kan barikin sojin kasar na 119 dake Mallam Fatori, jihar Borno.

Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, shi ne kwamandan runduna ta 272 mai kula da tankokin yaki.

Saboda jarumtarsa ne, a 2015 a Gamboru Ngala, babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya yi mushi karin girma daga Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai shekarun samun karin girman.

Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin kasa ta kasar, Kanar Sani Uman Kukasheka, ya ce sojojin sun kashe mayakan Boko Haram din goma sha hudu a lokacin artabun.

Ya ce wasu sojojin hudu kuma sun samu raunuka a harin wanda mayakan kungiyar suka kai a daren Juma'a.

Kanar Kukasheka ya ce cikin makaman da sojojin suka kwace daga wurin mayakan sun hada da babbar bindiga samfurin GPMG, da AK-47 guda bakwai da kuma albarusai da dama.

Kakakin sojin ya kuma ce ana ci gaba da aikin kakkabe mayakan Boko Haram din daga yankin.

A 'yan kwanakin nan dai, 'yan bindiga da ake gani mayakan Boko Haram ne sun yi ta yunkurin kai hare-hare a sassan jihar Borno da dama.

Ko a karshen watan Oktoba, sojojin Najeriyar biyar da 'yan sintiri uku da dan kato da gora daya sun rasa rayukansu lokacin da mayakan Boko Haram din suka yi musu kwanton bauna a kauyen Ugundiri dake karamar hukumar Damboa.

Sojoji sha tara kuma da dan kato da gora daya sun sami raunuka a kwanton baunar.

https://youtu.be/KhUBU4G1n0U

Asali: Legit.ng

Online view pixel