Mutane biyu sun rasu sakamakon hadarin mota

Mutane biyu sun rasu sakamakon hadarin mota

Mutane biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hadari daya afku a ranar Lahadin data gabata a garin gada-biyu dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito hadarin ya faru ne da misalin karfe 4 na yamma lokacin da wata mota kirar Corolla ta afka ma wata babbar motar Tirela.

Hadarin ya samu asali ne lokacin da direban Corollan ke sheka gudu a lokacin ana ruwa, daga nan ne motar ta kufce masa inda ya afka ma Tirelan dake ajiye a gefen hanya.

Mutane biyu sun rasu sakamakon hadarin mota

Wata majiya ta shaida cewa direban motar tare da abokin zaman shi ne suka mutu a hadarin, ya kara da cewa da kyar wasu mutanen garin suka iya curo shu daga cikin motar, inda suka wuce dasu asibitin Kwali, sai dai awanni kadan da kais u asibitin suke ca ga garinku.

KU KARANTA: Kotu ta daure shugaban karamar hukuma a gidan yari

Sai dai suma wasu daga cikin yan bada agajin sun rasa rayukansu yayin da birkin wata motar dakon mai ya tsinke, inda nan ma tayi kansu, take yanke mutane biyu suka rasu, inda da dama suka jikkata. Amma an garzaya da wadanda suka samu raunukan zuwa asibti domin duba lafiyarsu.

Da aka tuntubi shugaban hukumar kare haddura ta kasa wato FRSC na yankin Yangoji Amadi CO, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A wani labarin kuma, kimanin mutane 15 ne suka jikkata biyo bayan afka ma palwayan wutan lantarki da wata Tirela tayi a ranar Litinin 4 ga watan Oktoba a garin Abia. Hadarin ya faru ne lokacin da Tirelan take kan hanyarta ta zuwa garin Akwa Ibom ta afka ma wasu Palwayoyin wuta, inda ta take wasu direbobin Yar’kurkura su biyu da fasinjojinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng