Yan Najeriya sunyi martani ga Igwe kan gajeren wandon shi
Noble Igwe Sanannen mai amfani da dandalin sadarwa ne kuma wanda ya assasa kuma shugaban kungiyar 36o. Shi mai dinki ne kuma mai tasowa gun ado.
Shine wanda yake fitta da yadda za'a saka kaya a lokuttan biki, amma za'a iya Kiran shi mai daukar kasada in aka zo gurin ado, ranar lahadi 23 ga watan Oktoba yayi wata magana da wasu kayan gargajiya gajeru, da gajeren wando.
Ya saka hotunan shi guda 2 , a wasu kayan gargajiya da suke da gajeren wandon da be kai guiwa ba, yadda yayi shigan be zama wani sabon abu ba, amma saboda rashin tsawon wandon, da kuma yadda wandon ya matse shi, yasa mutane da yawa suna ganin be dace ba, suna Kiran wandon da suna gajeren wando maza.
Kalli hoto:-
Amma mabiyan shi a dandalin sadarwa sunyi tsokaci, wasu sun yaba, wasu sun kushe, wasu kuma tambayar shi sukayi.
Mouskicouto@Noble_ kayi kyau, amma wandon ya matse ka.
Pumpumjumee@ Noble_ sarkin gajeren wando.
Date is under@noble _ a matsayin ka na namiji be dace kasa wandon da be kaimaka guiwa ba.
Touchee@noble_ yayi kyau, amma ina matar da kasa wannan.
Asali: Legit.ng