Fitattun Ƴan Ƙwallon Afrika 5 da ba Su Taɓa Lashe Kofin AFCON ba

Fitattun Ƴan Ƙwallon Afrika 5 da ba Su Taɓa Lashe Kofin AFCON ba

Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) shi ne babban kofin kwallon kafa na maza a Afirka, wanda hukumar da ke kula da kwallon kafa ta Afirka (CAF) ke shirya wa.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gasar cin kofin AFCON tana tantance zakaran Afrika daga cikin kasashen da ke nahiyar, kuma tana daga cikin gasar kwallon kafa da aka fi kallo a duniya.

Fitattun 'yan wasan Afrika da ba su taba lashe kofin AFCON ba.
Mohamed Salah, Didier Drogba da suka shahara a taka leda amma ba su lashe kofin AFCON ba. Hoto: @MoSalah, @didierdrogba
Source: Twitter

'Yan wasan da ba su lashe AFCON ba

Zuwa yanzu, Masar ce kasar da ta fi samun nasara a tarihin AFCON, inda ta lashe kofin sau bakwai. Kamaru na biye da kofuna biyar, Ghana ta lashe guda hudu, yayin da Najeriya ta dauki kofin sau uku, cewar rahoton BBC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ake shirin gudanar da AFCON na 35 a Moroko daga 21 ga Disamba 2025 zuwa 18 ga Janairu 2026, Legit Hausa ta waiwayi wasu fitattun ‘yan wasan Afirka guda biyar da duk da bajintarsu, ba su taba lashe kofin AFCON ba.

Kara karanta wannan

EFCC ta cafke bokaye da kudin kasashen waje na boge bayan damfarar 'yan Najeriya

1. Mohamed Salah (Masar)

Mohamed Salah, fitaccen dan wasan Masar kuma mai taka leda a Liverpol.
Mohamed Salah, dan wasan kasar Masar da bai taba lashe kofin AFCON ba. Hoto: @MoSalah
Source: Twitter

A yayin da yake cikin shekararsa ta 33, ana fargabar lokaci na iya kurewa kyaftin din Masar, Mohamed Salah na daga kofin AFCON, domin sau biyu ya na samun nasarar yin hakan, a 2017 da kuma 2021.

Masar, wacce ita ce kasa mafi nasara a AFCON da kofuna bakwai, ta lashe kofin karshe a 2010 – kafin Salah ya yi fice sosai a matakin kasa da kasa.

Abin mamaki, Masar ba ta samu tikitin shiga gasar ba daga 2012 zuwa 2015, lamarin da ya jinkirta fitowar Salah a wasannin AFCON har zuwa 2017.

A shekarar, Masar ta sha kashi a hannun Kamaru a wasan karshe. A 2021 kuma, Masar ta sake kai wa wasan karshe amma ta sha kashi a bugun fenariti da Senegal.

A AFCON 2023, rauni ya hana Salah taka rawar gani, inda ya kalli fitar Masar daga zagaye na 16 daga gefe. AFCON 2025/2026 na iya zama damar karshe gare shi na cika burinsa na daga kofin.

Kara karanta wannan

Yadda Mikel Obi ya kira Buhari da kansa game da alawus a gasar kofin duniya

2. Didier Drogba (Ivory Coast)

Didier Drogba ya lashe kofuna a wasannin turai amma bai lashe kofin AFCON ba
Didier Drogba, dan wasan da ya yi tashe a Chelsea amma bai lashe kofin AFCON ba. Hoto: @didierdrogba
Source: Getty Images

'Yan wasa kadan ne suka taka leda son ransu kamar Didier Drogba. A wasannin Turai, kamar lokacin da yake buga wa Chelsea, ya shahara wajen ba da mamaki a wasannin karshe, tare da daga kofuna da dama, amma a AFCON, sa’a ba ta cimmasa ba.

Didier Drogba ya jagoranci Ivory Coast zuwa wasan karshe sau biyu – a 2006 da 2012 – inda bugun fenariti ya zama katangarsa daga lashe kofin AFCON din.

A 2006, ya rasa bugun fenariti yayin da Masar ta yi nasara. A 2012 kuma, ya buga fenariti sama da raga a karshen wasansu da Zambia, a nan ma Ivory Coast ta sake yin rashin nasara a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Abin takaici, Ivory Coast ta lashe AFCON a 2015, watanni kadan bayan Drogba ya yi ritaya daga buga wa kasar wasa.

3. George Weah (Liberia)

George Weah ya lashe Ballon d'Or amma bai lashe kofin AFCON ba
George Weah, tsohon shugaban kasar Liberia, kuma fitaccen dan kwallo da bai lashe AFCON ba. Hoto: @GeorgeWeahOff
Source: Depositphotos

George Weah shi ne dan Afirka daya tilo da ya taba lashe Ballon d’Or, inda ya samu wannan gagarumar lambar yabo a 1995, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.

Kara karanta wannan

Danyen mai ya yi faduwar da bai taba yi ba cikin shekaru 4 a kasuwar duniya

Dan wasan ya yi fice a kungiyoyi irin su Paris Saint-Germain da AC Milan, amma ya kasa samun nasarar daga kofin AFCON a kasarsa ta Liberia saboda karancin karfin kwallon kafar kasar.

Liberia ta samu damar shiga AFCON sau biyu ne kawai a lokacin Weah – a 1996 da 2002 – amma ba ta wuce matakin rukuni ba a kowanne karo. Weah ya zura kwallo daya ne kawai a AFCON, a wasan da suka tashi 1-1 da Mali a 2002.

Duk da rashin nasara a fagen kwallo, daga baya Weah ya jagoranci kasarsa ta wata hanya, inda ya zama shugaban kasar Liberia daga 2018 zuwa 2024.

4. Nwankwo Kanu (Najeriya)

Nwankwo Kanu na daga cikin fitattun 'yan Najeriya da suka shahara a buga kwallon kafa.
Nwankwo Kanu, dan wasan Najeriya da ya shahara a kwallon kafa, amma bai lashe AFCON ba. Hoto: @papilokanu
Source: Getty Images

Nwankwo Kanu ya yi fice a taka leda, inda ya lashe Champions League tare da Ajax da kuma manyan kofuna a Arsenal. A matakin kasa, ya lashe zinari a wasannin Olympics na 1996 tare da Najeriya.

Sai dai bai taba samun nasara a AFCON ba. Mafi kusa da ya kai ga kofin shi ne a 2000, lokacin da Najeriya ta kai wasan karshe. A wasan ta da Kamaru, Kanu ya barar da bugun fenariti, wanda ya sa Najeriya ta yi rashin nasara.

Kara karanta wannan

An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Najeriya ta kai wasan kusa da karshe sau hudu a zamaninsa, amma ba ta sake komawa wasan karshe ba. Kanu ya yi ritaya da lambobin azurfa da tagulla, amma ba da zinare a kofin AFCON ba.

5. Michael Essien (Ghana)

Michael Essien ya yi fice a kwallon kafa, amma bai tabuka abin kirki ga kasarsa Ghana ba.
Michael Essien, dan wasan Ghana da matsalolin lafiya suka hana shi lashe kofin AFCON. Hoto: @MichaelEssien
Source: Getty Images

Michael Essien ya kasance ginshikin kungiyar kwallon kafar Ghana bayan nasarar AFCON ta karshe da kasar ta samu a 1982. Kamar yadda ya yi fice a Chelsea, haka nan ya zama jagora a kungiyar Black Stars.

Amma rauni ya rika addabarsa a lokuta masu muhimmanci. Essien bai samu damar buga wasannin AFCON a 2006 ba, amma ya jagoranci Ghana zuwa matsayi na uku a 2008.

Rauni ya sake fitar da 'dan wasan tsakiyan daga AFCON 2010 yayin da Ghana ta kai wasan karshe, inda ta sha kashi a hannun Masar.

Matsalolin lafiya sun takaita buga kwallonsa, inda ya shiga jerin manyan ‘yan wasan Afirka da iya taka ledarsu bai taba kai su ga lashe kofin AFCON ba.

Ahmed Musa ya yi ritaya daga kwallo

A wani labari, mun ruwaito cewa, Kyaftin Ahmed Musa ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa a matakin kasa bayan shafe shekaru 15 yana wakiltar Najeriya.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Borno da wani ya tashi bam, ya kashe sojojin Najeriya

'Dan wasan wanda ya kasance cikin tawagar da ta lashe kofin AFCON a 2013, ya gode wa masoyansa a gida da wajen Najeriya bisa goyon bayan da suka ba shi.

Ahmed Musa ya wakilci Najeriya a tawagar ’yan kasa da shekaru 20 (U20) da 23 (U23) a farkon fara taka ledarsa, tare da buga wasa a kungiyoyi da dama a kasashen waje.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com