Shugaba George Weah na Liberiya ya yanke wa kansa albashi
- Shugaban Liberia Goerge Weah ya tabbatar da cewa kasar tana cikin matsalar tattalin arziki
- Yayi alkawarin kawo karshen cin hanci da rashawa
- Sannan ya kuma yi alkawarin bada aikin hanya na dala billion 3 wanda zai kai har cikin babban birnin
Shugaba Goerge Weah na kasar Liberia yayi alkawarin yanke albashin sa da kashi 25 cikin 100 a ranar litinin dinnan data gabata, 29 ga watan Janairu, a jawabin da yayi a wani taro, inda yace al’ummar kasar suna fama da wahalar rayuwa.
A jawabin sa tsohon dan wasan kwallon kafar ya kara da cewar zai yi hakan ne domin rage wahalar rayuwa da al’ummar kasar ke fama dashi. Shugaban kasar Liberian yana samun kimanin dala 100,000 a kowace shekara, hakan na nufin cewa shugaba George Weah zai rage dala 25,000.
DUBA WANNAN: Sabon shugaba Weah ya yankawa kansa albashi
Weah yace: “tattalin arzikinmu ya karye, rashin aikin yi yayi yawa, kasashen mu basu da tasiri a kasashen waje”. Weah yayi alkawarin kawo karshen cin hanci da rashawa, a jawabin da yayi lokacin da ake rantsar dashi, a babban birnin kasar.
Tun bayan lashe zaben, tsohon dan wasan AC Milan da kuma Paris St. Germain, yana cikin jimami da irin halin da kasar take ciki. Sannan yayi alkawarin domin ganin ya habaka tattalin arzikin kasar. Ya kara da tabbatar wa da yan kasar cewa ba tare da bata lokaci ba, zai rage kasha 25 daga albashin sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng