Yadda tsohon ‘Dan kwallon Duniya ya lashe zaben Shugaban Kasa

Yadda tsohon ‘Dan kwallon Duniya ya lashe zaben Shugaban Kasa

- George Weah ya kafa tarihi inda zai mulki Kasar Liberia

- Weah ya taba zama na farko a Duniya wajen buga tamule

- Tsohon ‘Dan wasan ya ba Boakai kashi a zaben da aka sake

Tsohon ‘Dan wasan Duniya George Weah ya kara kafa tarihi inda zai mulki Kasar sa bayan ya ajiye kwallon kafa. Dama shi kadai ne ‘Dan wasan Afrika da ya taba zama gwarzon Duniya.

Yadda tsohon ‘Dan kwallon Duniya ya lashe zaben Shugaban Kasa
Tsohon ‘Dan kwallon AC Milan ya ci zabe

A wannan rana kuma mun kawo manyan abubuwan da ya kamata ka sani game da tsohon ‘Dan wasan da zai zama Shugaban Kasar Liberia idan Shugaba Allen Johnson Sir-Leaf ta kammala wa’adin ta.

KU KARANTA: Wani Sanatan Kano na bayan Shugaba Buhari ya zarce

Yadda tsohon ‘Dan kwallon Duniya ya lashe zaben Shugaban Kasa
Arsene Wenger ya fara shigo da Weah cikin Turai

1. Arsene Wenger ya fara shigo da George Weah cikin harkar kwallon kafan Turai a shekarar 1988.

2. Daga Monaco, Dan wasan ya wuce Kungiyar PSG inda yaci kofin Gasar gida da na Turai na UEFA.

3. Bayan nan ‘Dan wasan gaban ya zarce zuwa A.C Milan inda har ya zama gwarzon Duniya a can.

4. Daga Kasar Italiya sai Weah ya koma Ingila inda ya bugawa irin su Chelsea da su Manchester City

5. ‘Dan wasan ya komo inda ya fara wasa watau Faransa a 2001 inda ya bugawa Kungiyar Marseille.

6. George Weah ya koma Kasashen Larabawa watau Kungiyar Al-Jazira da wasa kafin ya ajiye kwallo.

7. Babban ‘Dan wasan ya bugawa Kasar sa kwallo har ya ci kwallaye 22 kuma har ya je Gasar Afrika.

8. Sai dai ‘Dan wasan bai taba buga wasan cin kofin Duniya ba watau World Cup har ya ajiye wasa.

9. Yayi takara da Shugaban Kasa mai ci a baya amma ya sha kasa don haka ya koma karo ilmi.

10. A shekarar 2014 ya zama Sanatan Kasar yanzu kuma ya lashe zaben Shugaban Kasa a karo na biyu.

Tsohon ‘Dan wasan ya ba Joseph Boakai kashi kwarai a zaben da aka sake kwanan nan. Sai dai ana kishin-kishin din cewa Mataimakiyar sa za ta zama Matar tsohon Shugaban Kasar Charles Taylor ne da ke gidan kurkuku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng