Abubuwa 10 game da tsohon wasa Kanu Nwankwo

Abubuwa 10 game da tsohon wasa Kanu Nwankwo

– Tsohon dan wasan Super Eagles, Kanu Nwankwo ya cika shekaru 40 da haihuwa.

– An haifi Tauraron dan wasan na Najeriya Kanu ne a ranar 1 ga watan Agusta.

– Legit.ng ta kawo maku abubuwa goma dangane da dan wasa Kanu.

Abubuwa 10 game da tsohon wasa Kanu Nwankwo

 

 

 

 

An haifi tsohon dan wasan Najeriya Kanu Nwankwo a ranar Tsohon da ga watan Agustan 1976. Ya buga ma Kungiyoyi da dama, kamar su Ajax, Inter Milan, Arsenal, Wes Brom, da kuma Portsmouth. Najeriya dai ba ta taba samun dan wasa irin Kanu Nwankwo ba. Ga wasu abubuwa da suka shafi dan wasan da watakila ba ka taba sani ba:

1. Kungiyar Arsenal ta Ingila ta lissafa Kanu a cikin matsayin babban dan wasan ta na 13 a tarihi a watan Feburairu 2016. Cikin yan wasa 50 da aka fitar a kulob din, Kanu ya zo na 13.

Kanu na cikin manyan yan kwallon duniya da Hukumar kula da tarihin kwallon duniya, IFFHS ta karkashin Kungiyar FIFA ta fitar.

A shekarar 2007 Kungiyar AFS ta saka Kanu Nwankwo cikin manyan yan kwallon duniya 100 da ake da su. Dan wasan ya zo na 76 a jeringiyar.

Kanu ne zakaran dan wasan Afrika a shekarar 1996 da kuma 1999, kuma shine dan Najeriya na karshe da ya lashe kyautar na gwarzon Afrika.

Kanu ya samu cin kofin UEFA Champions League, UEFA Cup, Premier league (har sau biyu), FA Cups (Sau 3) da kuma kofin Olympics.

Kanu yana bin kulob din san a Portsmouth kudi har fam miliyan £3, sai dai ya hakura ya yafe saboda halin da Kungiyar ta shiga ciki.

Anyi masa aiki a zuciyar sa a shekarar 1996, inda yayi doguwar jinya, bayan nan kuma an kara duba lafiyar zuciyar na sa a shekarar 2014.

Kanu ya buga ma gida Najeriya wasanni 86, hakan na nufin yan wasa biyu kadai suka fi sa yawan wasanni a tarihi; Yobo da Enyeama.

Kanu ya auri matar sa Amara a shekarar 2004 lokacin tana shekara 18 da haihuwa. Suna da ‘ya ‘ya 3 tare.

Kanu Nwankwo ne dan wasa na 3 cikin wadanda suka fara buga wasa daga bisa benci a Tarihin Premier League.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng