Gasar UEFA: Osimhen da Wasu Manyan Ƴan Wasan Najeriya 4 da za a Kalla a 2025/26

Gasar UEFA: Osimhen da Wasu Manyan Ƴan Wasan Najeriya 4 da za a Kalla a 2025/26

Gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League) ta dawo, kuma kamar koyaushe, za ta faranta ran wasu, ta kuma bakanta ran wasu, wani yanayi da masoya kwallon kafa ke fuskanta a duk kaka.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ga ‘yan Najeriya, kakar UEFA ta 2025/26 za ta fi kowane lokaci daukar hankali saboda akwai manyan ‘yan wasan kasar biyar da za su buga wasanni a kungiyoyi daban daban.

'Yan wasan Najeriya 5 za su taka leda a kakar wasanni ta Zakarun Turai ta 2025/2026.
Hoton Victor Osimhen, da Ademola Lookman, suna taka leda a kungiyoyi daban daban. Hoto: @Alookman_, @victorosimhen9
Source: Getty Images

Najeriya ta daɗe tana kafa tarihi a gasar UEFA, tun daga lokacin da Nwankwo Kanu da Finidi George suka lashe kofin tare da Ajax, zuwa lokacin John Obi Mikel ya dauki kofin da Chelsea a 2012, cewar rahoton Tribune.

Yanzu sababbin taurari ne ke jan ragamar kasar a Turai, inda suke cike da burin faranta ran masoya kwallon kafa, da kafa nasu tarihin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta hakura da lafta sabon harajin shigo da layayyaki Najeriya

A wannan rahoto, mun jero 'yan wasan Najeriya biyar da ake sa ran kallo a kakar wasannin Zakarun Turai ta 2025/2026:

1. Victor Osimhen

Victor Osimhen zai fafata a Galatasaray, bayan da ya yi nasarar taimaka wa kungiyar ta dawo gasar Zakarun Turai.
Fitaccen dan wasan Najeriya, kuma zakara a kungiyar Galatasaray, Victor Osimhen. Hoto: @victorosimhen9
Source: Getty Images

Yayin da ya taimaka wa sabuwar kungiyarsa, Galatasaray, ta dawo gasar Zakarun Turai, yanzu idanu sun koma kan Victor Osimhen, tsohon gwarzon dan wasan Afrika, ana jira a kaga bajintarsa da zai nuna a babbar gasar ta Turai.

Galatasaray za ta fafata da manyan abokan hamayya irin su Liverpool, Man City, Atletico Madrid, Monaco, da Ajax.

Ana ganin hakan zai ba magoya bayan Osimhen damar ganin cikakkiyar kwarewarsa a taka leda, idan ya hadu da manyan kungiyoyin kwallon kafar.

2. Ademola Lookman

Masu kallon kwallon kafa na da burin ganin Ademola Lookman ya taka leda a kakar wasanni ta Zakarun Turai a bana.
Hoton gwarzon dan wasan Afrika, kuma dan wasan Atalanta, Ademola Lookman. Hoto: @Alookman
Source: Getty Images

Ademola Lookman bai buga wasanni a wasannin shirye-shiryen kakar wasa tare da Atalanta tun bayan karshen kakar 2024/25 ba, sakamakon tsaikon da aka samu na zuwansa Inter Milan.

Duk da hakan, magoya bayansa daga Najeriya suna sa ran ganin irin bajintar da gwarzon dan wasan Afrika na yanzu zai taka a wasansa da Paris Saint-Germain a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Ranar Lahadi: Za a sheka ruwan sama a Kebbi, Sokoto, Zamfara da jihohin Arewa 12

Sai dai, wani rahoto na jaridar Punch ya nuna cewa, ba lallai Lookman ya taka leda a wasan Atalanta da PSG ba, inda kocin ke ci gaba da barinsa a benci saboda yunkurin da ya yi na barin kungiyar.

3. Nathan Tella

'Yan Najeriya na jira su ga irin rawar da Nathan Tella zai taka a gasar Zakarun Turai ta 2025/2026
Nathan Tella, dan wasan Najeriya da ke buga kwallo a kungiyar Bayern Leverkusen. Hoto: @433
Source: Getty Images

Nathan Adewale Temitayo Tella dan wasan Najeriya ne wanda tsohon kocin Najeriya, José Peseiro, ya gayyace shi a ranar 10 ga Nuwamba, 2023, don shiga wasannin share fage na gasar cin kofin duniya na 2026 da Lesotho da Zimbabwe.

A matsayinsa na wani bangare na tawagar Bayern Leverkusen da ta lashe kakar Bundesliga ta 2023/2024, masu kallon kwallo a Najeriya suna tsumayin ganin Tella ya fara buga gasar Zakarun Turai.

4. Raphael Onyedika

Raphael Onyedika, zai buga wa Club Burgge wasa a kakar wasanni ta Zakarun Turai ta 2025/2026
Raphael Onyedika, dan wasan Najeriya da ke buga wa kungiyar Club Burgge na taka leda a cikin fili. Hoto: @lemarcaspors_/X
Source: Getty Images

Kungiyar da Onyedika ke buga wa wasa, Club Brugge za ta fuskanci AS Monaco a gasar Zakarun Turai ta wannan kakar a ranar Alhamis, cewar rahoton shafin UEFA.

Ana sa ran dan wasan Najeriyar, Raphael Onyedika zai yi iya yinsa don zama abin kallo a wasan, a kokarinsa na samun nasara a Turai.

5. George Ilenikhena

George Ilenikhena zai buga wa AS Monaco wasa, inda zai taka leda a kakar Zakarun Turai ta 2025/2026
George Ilenikhena, fitaccen dan wasan Najeriya da ke buga wasa a kungiyar AS Monaco. Hoto: @Ligue1_ENG
Source: Getty Images

Yayin da kungiyar Faransa ta AS Monaco ke shirin buga wasa da Club Brugge a ranar Alhamis a wasansu na gasar Zakarun Turai, shi ma George Ilenikhena zai yi fatan samun nasarar jan hankalin jama'a kansa, yayin da zai fuskanci ɗan ƙasarsa, Raphael Onyedika.

Kara karanta wannan

Yawan rayuka da aka rasa a Gaza bayan mummunan harin da Isra'ila da ta kai

'Yan wasan Najeriya 15 mafi albashi a Turai

A wani labarin, mun rahoto cewa, Najeriya ta na da zakakuran ‘yan wasa da suka yi fice a harkar kwallon kafa a duniya baki daya.

A bangaren kwasar albashi, Victor Osimhen, wanda ya buga wa Napoli da ke Italiya wasa, shi ne yafi kowa samun kudi, inda yake karbar akalla fan 167,000 a ko wane mako.

Samuel Chukwueze shi ne na biyu a jerin masu kwasar kudi a Najeriya inda ya ke samun fan 84,413 a mako, a kungiyar kwallon kafa ta AC Milan da ke kasar Italiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com