Man City tayi abin da ba a taba yi ba a tarihin kwallon Ingila
A bana dai Kungiyar Manchester City ce ta lashe Gasar Firimiya na Ingila. Kocin Kungiyar Pep Guardiola ya samu lambar yabo daga ko ina a Duniya bayan ya kafa wasu tarihi da zai yi wahala a iya doke su kwanan nan.
Mun tattaro wasu daga cikin tarihin da Manchester City ta kafa a gasar wannan shekarar wanda su ka hada da samun makin da babu wanda ya taba lashewa a gasar.
1. Maki 100 a Gasar BPL
Tun da aka fara Gasar Firimiya ba a taba samun Kungiyar da ta tashi da maki 100 a shekara guda ba sai Man City a bana.
2. Yawan kwallaye
Adadin kwallayen da City ta dirka a raga ma dai ya shiga tarihi don kuwa a bana sai da Man City ta jefa kwallaye 105 a Ingila.
KU KARANTA: Ba mamaki Tsohon ‘Dan wasan Arsenal ya zama sabon Koci
3. Nasarori a waje da gida
Haka kuma idan ana maganar samun nasara a wajen gida babu wanda ya taba yin abin da Guadiola yayi. City ta ci wasanni 16 da ta buga ba a gida ba.
4. Nasarori a jere
Ban da cewa Man City ta ci wasanni 16 a waje da gida, Guardiola ya kuma yi wasanni 18 a jere yana cin wasanni ba tare da an taka masa burki ba.
5. Rarar kwallaye
An rufe teburin Firimiya ne dai Manchester City ta na da rara kwallaye 79. Babu kulob din da ya taba samun wannan nasara a Gasar Firimiya.
6. Rata a saman tebur
Haka kuma ba a taba samun zakarun da su ka ba na biyu a teburin Firimiya ratar maki 19 ba. Man United dai ta kare ne da maki 19 a bayan Makwabatan ta
.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng