Tawagar Yan Wasan Najeriya Ta Naɗa Dalibin Sakandare a Matsayin kyaftin

Tawagar Yan Wasan Najeriya Ta Naɗa Dalibin Sakandare a Matsayin kyaftin

  • Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya 'yan kasa da shekaru 17 ta nada dalibin makarantar sakandare a matsayin kyaftin dinta
  • Golden Eaglets da ke wakiltar Najeriya a matakin yan kasa da shekaru 17 ta zabi Simon Cletus a matsayin kyaftin
  • Wannan na zuwa ne yayin da tawagar ta shirya buga wasa domin neman gurbi a gasar AFCON da za a yi a kasar Ghana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ƴan kasa da shekaru 17 ta nada ɗalibin sakandare kyaftin dinta.

Tawagar ƴan wasan Najeriya ta Golden Eaglets da ke wakiltar Najeriya ta zabi Simon Cletus a matsayin kyaftin mai rike da kambu.

Kara karanta wannan

Babu Bahaushe ko 1: Jerin manyan mawaka 10 mafi arziki a Nigeria a 2024

Dalibin sakandare ya zama kyaftin din tawagar Golden Eaglets a Najeriya
Tawagar Golden Eaglets ta nada dalibin sakandare, Simon Cletus a matsayin kyaftin. Hoto: @OgaNlaMedia.
Asali: Twitter

Golden Eaglets ta nada kyaftin

Complete Sport ta tattaro cewa tawagar za ta kara da Burkina Faso a gasar neman gurbin shiga AFCON na 'yan kasa da shekaru 17.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a buga wasan ne a gobe Alhamis 16 ga watan Mayu domin neman gurbin a gasar da za a yi a kasar Ghana.

Tawagar Golden Eagles ta na rukunin B ne da kasashen Burkina Faso da Togo da kuma Jamhuriyar Nijar.

A wace kungiya Cletus ke buga wasa?

Cletus ya na buga wasa ne a kungiyar ƙwallon kafa ta Mavlon a matsayin dan wasan gaba, kamar yadda SoccerNigeria ta ruwaito.

Shi da 'dan wasan ya kasance kwararren 'dan kwallo wanda ke cin kwallaye kuma ya ke samar da hanyoyin cin ƙwallo a cikin wasa.

Wannan kwarewar tasa za ta tabbatar da kokarin da Golden Eaglets za ta yi a gasar da za a yi a kasar Ghana.

Kara karanta wannan

Matar ɗan Sarkin Ingila, Harry ta ji dadin Najeriya, ta ce ta samu gida

Mbappe ya sanar da barin PSG

A wani labarin, fitaccen ɗan wasan kwallon ƙafa, Kylian Mbappe ya sanar da barin ƙungiyar ƙwallon ƙafan ta Paris Saint-Germain (PSG) a karshen kaka.

Mbappe ya bayyana cewa zamansa ya zo ƙarshe a PSG a wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta a ranar Jumu'a 10 ga watan Mayu.

Babban ɗan wasan mai buga tamaula a gaba ya tabbatar da zai bar PSG a bidiyon da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel