An Haramta Wa Ƴan Ƙwallo Musulmi Yin Azumi a Faransa, Wani Ɗan Wasa Ya Ɗauki Mataki

An Haramta Wa Ƴan Ƙwallo Musulmi Yin Azumi a Faransa, Wani Ɗan Wasa Ya Ɗauki Mataki

  • Wani ɗan wasan gaba na tawagar kwallon kafa ta kasar Faransa, Mahamadou Diawara, ya fice daga tawagar saboda an haramta masu yin azumi
  • Hukumar kwallon kafa ta Faransa (FFF) ta kafa dokar haramta wa ƴan wasa Musulmi yin azumi ma damar suna buga wa ƙasar kwallo
  • Ba iya Diawara kadai ba, ƴan kwallon da Musulmai ne sun nuna adawa kan wannan dokar wacce suke ganin ba ta girmama addininsu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Faransa - Dan wasan ƙwallon ƙafa, Mahamadou Diawara, ya fice daga tawagar ƴan ƙasa da shekaru 19 na ƙasar Faransa.

Diawara ya dauki wannan matakin ne bayan da ya gano cewa hukumar kwallon kafa ta Faransa (FFF) ta haramtawa ƴan wasa Musulmi yin azumin watan Ramadan.

Kara karanta wannan

NEC: Gwamnoni 16 sun goyi bayan ƙirkiro ƴan sandan jihohi domin dawo da zaman lafiya

Dan wasan Faransa ya hakura da buga kwallo saboda an hana shi yin azumi
Ramadan: Faransa ta kakaba dokar hana 'yan kwallo Musulmi yin azumi. Hoto: @M_dwr8
Asali: Twitter

Jaridar ESPN ta ruwaito cewa Diawara bai ji dadin wannan mataki na hukumar ba, wanda ya tilasta shi hakura da buga wasa a tawagar tare da komawa tawagarsa ta gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Faransa ta hana 'yan wasa yin azumi

Hukumar FFF ta tabbatar da ficewar Diawara daga babbar tawagar ƙasar, tare da maye gurbinsa da ɗan wasa Dehmaine Tabibou Assoumani.

Kamar yadda ya zanta da jaridar Le Figaro a ranar Laraba, shugaban hukumar FFF, Philippe Dialo, ya ce doka ce ga ƴan wasa ba za su kawo addini a harkar kwallon kafa ba.

Dokar hukumar FFF ta yi nuni da cewa ƴan wasan da aka kira su don buga wa tawagar ƙasar kwallo ba za suyi azumin Ramadan ba, kuma dole su bi tsare-tsaren hukumar.

'Yan wasa sun yi wa Faransa adawa

Rahoton jaridar ABC News ya yi nuni da cewa 'yan wasa Musulmi, wadanda suka fara azumin Ramadan daga ranar 10 ko 11 ga watan Maris, za su sha ruwa a ranar 10 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Dikko Radda: Gwamnan Katsina da ya ce ba zai yi sulhu da ƴan bindiga ba

Wani wakilin ƴan wasa a tawagar Faransa, ya bayyana cewa:

"Ƴan wasa Musulmi sun nuna adawa kan wannan dokar. Suna ganin ba a martaba addininsu ba, wannan ya sa Mahamadou ya hakura da buga wasan."

Kocin Najeriya, Peseiro, ya ajiye aiki

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa mai horas da ƴan wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya (Super Eagles), Jose Peseiro, ya ajiye aiki bayan ƙarewar wa'adin kwantiraginsa.

Akalla watanni 22 Peseiro ya shafe a matsayin kocin Super Eagles, Kuma ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa wasan ƙarshe a gasar kofin AFCON 2023/2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.