FIFA ta Hana Indiya Shiga Kwallo, An Kawo Hujjar Dakatar da Kasar a Duniya

FIFA ta Hana Indiya Shiga Kwallo, An Kawo Hujjar Dakatar da Kasar a Duniya

A Yau ne Hukumar kwallon kafa na FIFA ta dauki mataki a kan kungiyar All India Football Federation

FIFA ta dakatar da AIFF ne saboda an tsoma baki a kan shugabancin kungiyar wasan kwallon Indiyar

A dalilin wannan, zai yi wahala a bar kasar Ingila ta dauki nauyin gasar U-17 na mata da za ayi a 2022

Zurich - Hukumar kwallon kafa na FIFA ta Duniya ta dakatar da kungiyar All India Football Federation (AIFF), ba tare da wani bata lokaci ba.

Kamar yadda FIFA ta wallafa a shafinta na yanar gizo dazu, an dauki wannan mataki a kan kungiyar kwallon kafan ne saboda katsalandan.

Sanarwar da aka fitar a ranar Talata ta nuna akwai yiwuwar a dakatar da kungiyar kwallon kafa na mata, wanda zai iya kawowa Indiya cikas.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Nada Dangote Wata Mukami Mai Muhammanci a Najeriya

A watan Oktoban nan aka tsara za a buga gasar cin kofin Duniya na mata ‘yan kasa da shekara 17, kasar Indiya aka ba dawainiyar shirya gasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin kungiyar kwallon matan kasar da laifin sabawa tsarin da FIFA ta amince da shi.

An yi wa AIFF katsalandan

Jawabin da hukumar Duniyar ta fitar ya nuna gwamnati ta tsoma baki a kan sha’anin kungiyar AIFF, wannan katsalandan ya sabawa ka’ida.

FIFA.
Hedikwatar FIFA Hoto: www.tripadvisor.com
Asali: UGC

Ba za a janye dakatarwar ba, sai an ruguza kwamitin rikon kwarya da aka kafa su kula da aikin AIFF, a dawo da asalin shugabannin kungiyar.

A halin yanzu an samu baraka a kungiyar kwallon, an gagara shirya zaben sababbin shugabanni. Hakan ya jawo aka sabawa tsarin dokar AIFF.

Kwamitin rikon kwarya

A watan Mayun 2022 kotun koli ta sauke shugabannin AIFF, ta nada wani kwamitin rikon kwarya na mutum uku da za su shirya zaben da ake jira.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari: APC ta gyara kasar nan, kamar ba a taba ta'addanci ba

Alkalan Babban kotun kasar Indiyar sun umarci a gudanar da zaben sababbin shugabannin kungiyar kwallon kafan a karshen watan Agusta.

Da wannan dakatarwar da aka yi kungiyar, CNN ta rahoto cewa ba zai yiwu a buga gasar U-17 a Indiya tsakanin 11 da 30 ga watan Oktoban bana ba.

Rahoton yace shugabannin FIFA su na duba halin da ake ciki, za a kai maganar zuwa gaban majalisarta domin ganin ko za a janye gasar daga kasar.

Cinikin Neymar ya tashi

A watan Yuli aka samu rahoto cewa Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa na PSG, Neymar Jr. zai je kotu a kan tashinsa daga Santos a 2013.

Wata kungiya a Brazil ta shigar da kara, tace an boye gaskiyar cinikin da aka yi da Barcelona a lokacin. A kan wannan maganar za ta koma kotu.

Kara karanta wannan

A shirye muke: ASUU sun sauko, sun ce za su iya janye yaji a yau bayan ganawa da FG

Asali: Legit.ng

Online view pixel