Kocin Kungiyar Kwallon Ƙafa Ta Najeriya Super Eagles Ya Yi Murabus, Ya Faɗi Dalili

Kocin Kungiyar Kwallon Ƙafa Ta Najeriya Super Eagles Ya Yi Murabus, Ya Faɗi Dalili

  • Kocin tawagar ƴan wasan Najeriya, Jose Peseiro, ya aje aiki bayan kwantiragin da ya rattaɓa wa hannu ya ƙare jiya Alhamis, 29 ga watan Fabrairi
  • Peseiro ya bayyana tsawon watanni 22 da ya shafe a matsayin kocin Super Eagles da abun alfahari da girma a rayuwarsa
  • Ya gode wa shugaban hukumar kwallon ƙafa NFF, ma'aikata da ƴan wasan Super Eagles, waɗanda ya jagoranta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mai horarwa, Jose Peseiro, ya kammala aikinsa a matsayin kocin ƙungiyar kwallon ƙafa ta Najeriya watau Super Eagles.

Peseiro, ɗan asalin kasar Fotugal ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo: An samu hanyar da za a kawo karshen 'yan bindiga a Najeriya

Tsohon kocin Najeriya, Jose Peseiro.
Kocin Super Eagles, Jose Peseiro, Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa, Ya Fadi Daili Hoto: Jose Peseiro
Asali: Getty Images

A cewarsa, kwantiragin da ya rattaɓa wa hannu da hukumar kula da harkokin kwallon ƙafa ta Najeriya (NFF) ya ƙare daga ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai horas da ƴan wasan kwallon ƙafan ya ce:

"A jiya muka karkare kwantiragi na da NFF, abun alfahari ne da girma a wurina da na horas da Super Eagles. Watanni 22 kenan da ke cike da sadaukarwa, ina jin gamsuwa a raina."

Kocin ya miƙa sakon godiya

Peseiro ya miƙa godiyarsa ga shugaban NFF da ya ɗauke shi aiki, ma'aikatan hukumar kwallon ƙafa da ɗaukacin ƴan wasan Super Eagles karƙashin kaftin Ahmed Musa.

"Muna mika godiyarmu ga Sir Amaju Pinnick (shugaban da ya ɗauko mu muka sa hannu), Shugaba Ibrahim Gusau, babban sakatare, Mohammed Sanusi, sakatare, Dayo Enebi.
"Mun kuma gode wa hukumar NFF da dukkan ma'aikatanta musamman ƴan wasa gaba ɗaya, waɗanda nake alfahari da jagorantar su.

Kara karanta wannan

CBN: Babban banki ya soke lasisin ƴan canji sama da 4,000, ya faɗi muhimmin dalili

"Jama'a muna godiya, ba ƙaramar alfarma bace zama ɓangaren wannan dangi, zamu yi kewarku amma a koɗa yaushe muna tare da ku a duk inda kuka tsinci kanku."

- Jose Peseiro.

Wace rawa ya taka a matsayin kocin Super Eagles?

Kocin mai shekaru 63 ya karɓi jagorancin kungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya a watan Yunin 2022 bayan Super Eagles ta kasa samun gurbi a gasar cin kofin duniya.

Ya jagoranci Najeriya ta lashe lambar azurfa a gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON 2023). Ana alaƙanta Peseiro da aikin kocin ƴan wasan Algeria.

Jerin ƴan wasan Najeriya da suka fi kwasar kuɗi

A wani rahoton kun ji cewa Najeriya ta na da zakakuran matasan ‘yan wasa da suka yi fice a harkar kwallon kafa a duniya baki daya.

Legit Hausa ta jero muku sunayen ‘yan wasan guda 15 da suka fi samun kudade a ƙungiyoyin da suke murza leda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel