Hukumar Kwallon Kafa Ta Saudiyya Ta Dakatar da Ronaldo da Cin Tararsa Kan Dalili 1, an Yaɗa Bidiyon

Hukumar Kwallon Kafa Ta Saudiyya Ta Dakatar da Ronaldo da Cin Tararsa Kan Dalili 1, an Yaɗa Bidiyon

  • Fitaccen dan wasan kwallon kafa a duniya, Cristiano Ronaldo ya shiga matsala kan wani nuni na rashin da'a da ya yi a Saudiyya
  • Hukumar kwallon kafa ta kasar ce ta dakatar tare da kuma cin tararsa kan nuna rashin da'a da ya yi a wasan da aka gudanar
  • Har ila yau, hukumar bayan dakatar da shi ta kuma ci tararsa dala dubu takwas ba tare da daukaka kara ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Riyal, Saudiyya - Hukumar kwallon kafa ta Saudiyya ta dakatar da fitaccen dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo.

Hukumar ta dakatar da dan wasan ne wasa daya saboda wani abu da ya yi da ke nuna rashin da'a a wasan da aka gabatar a karshen mako.

Kara karanta wannan

A fadi illar da Kiripto ke yi wa tattalin arziki yayin da aka cafke shugabannin Binance, za a haramta

An dakatar da Ronaldo kan nuna rashin da'a a Saudiyya
Bayanan Ronaldo ba su wanke shi daga zargin ba. Hoto: @cristiano.
Asali: Instagram

Menene dalilin cin tarar Ronaldo?

Har ila yau, hukumar ta ci tarar Ronaldo dala dubu takwas kan kawo tsaiko da tashin hankali a yayin wasan, cewar Sportbible.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dokar da kuma ce dole Ronaldo zai yi biyayya ga hukuncin saboda ba zai iya daukaka kara kan matakin ba, cewar Punch.

A wasan da kungiyar Al-Nassr ta buga da Al-Shabab an gano a cikin faifan bidiyo dan wasan ya na nuni ta rashin da'a ga wani bangare na magoya bayan.

Martanin da Ronaldo ya yi kan zargin

Ronaldo ya yi hakan ne don mayar da martani yayin da suke kiran sunan Lionel Messi wanda babban abokin hamayyarsa ne, talksport ta tattaro.

Ronaldo daga bisani ya ce abin da ya yi ya na nuna jarunta ne da nasara ba da wata manufa ba inda ya ce a Nahiyar Turai hakan ba matsala ba ne.

Kara karanta wannan

Yayin da 'yan Najeriya ke fatan juyin mulki, Sojoji sun tura sako ga 'yan kasar kan muhimmin abu 1

Ya ce:

"Ina mutunta dukkan kungiyoyi, murnar da na ke yi alamu ne na kwarin gwiwa da nasara, ba abin kunya ba ne mun saba da haka a Nahiyar Turai."

Musa ya yi magana kan makomarsa

Kun ji cewa dan wasan Super Eagles, Ahmed Musa ya yi martani kan makomarsa a tawagar bayan kammala gasar AFCON.

Kyaftin din tawagar ya ce har yanzu shi dan kwallo ne duk lokacin da aka bukaci ya zo ya ba da gudunmawa zai amsa gayyata.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ta cece-kuce da rashin buga wasa ko sau daya da Musa ya yi a gasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel