AFCON 2023: Jerin Kasashe 2 Da Super Eagles Za Ta Iya Karawa Da Su a Wasan Kusa Da Na Karshe

AFCON 2023: Jerin Kasashe 2 Da Super Eagles Za Ta Iya Karawa Da Su a Wasan Kusa Da Na Karshe

  • Super Eagles ta Najeriya ta samu galaba a kan Palancas Negras na Angola da ci 1-0 a gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) 2023
  • Ademola Lookman ne ya zura kwallon a ragar Angola da ya ba Najeriya damar ta tsallake zuwa matakin kusa da na karshe a karo na 15
  • Yanzu suna jiran wanda zai yi nasara tsakanin Cape Verde da Afrika ta Kudu domin tantance abokiyar karawarsu a wasa na gaba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abidjan, Ivory Coast - Super Eagles ta Najeriya ta tsallake zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake gudanarwa a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

FAAN: Ministan Tinubu ya bayyana alfanun da za a samu kan mayar da ofishin Legas, ya fadi dalili

Najeriya ta samu nasarar ne bayan da ta doke Palancas Negras ta Angola da ci 1-0 a Abidjan a ranar Juma'a 2 ga Fabrairu.

Cape Verde ko Afrika ta Kudu: Kasar da Najeriya za ta kara da ita a 'semi final'
Cape Verde ko Afrika ta Kudu: Kasar da Najeriya za ta kara da ita a 'semi final'. Hoto: @BafanaBafana, @NGSuperEagles
Asali: Twitter

Super Eagles dai ta yi aiki tukuru domin samun nasara a kan kungiyar Palancas Negras, wadda ta bada mamaki na yadda ta kai wasan daf da na kusa da na karshe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kokarin da Super Eagles suka yi

Najeriya ce ta mamaye zagayen wasan na farko, inda dan wasan Napoli Victor Osimhen ya hana masu tsaron gidan Angola katabus.

Ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, Moses Simon ya wurgawa Lookman kwallo, wanda shi kuma ya zura ta a ragar Guilherme da Costa.

Angola ta kusa ramawa bayan an dawo daga hutun rabin lokaci inda dan wasa Abrosini Salvador ya so jefa kwallo a ragar Najeriya amma ta bugi karfe.

Kara karanta wannan

AFCON 2023: Tinubu ya yi magana da tawagar Super Eagles gabanin karawa da Angola

Har ila yau, Osimhen ya zura wata kwallo a ragar Angola ta bugun kai, amma mai hura wasan ya kashe kwallon ta dalilin shigar Osimhen 'offside'.

AFCON 2023: Da wa Najeriya za ta fafata a wasan kusa da na karshe?

Najeriya za ta kara da wadda ta yi nasara a wasan daf da na kusa da na karshe tsakanin Cape Verde da Afrika ta Kudu domin samun tikitin zuwa wasan karshe.

Za a buga wasan daf da na kusa da na karshe ne a ranar Asabar 3 ga watan Fabrairu, kamar yadda hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF ta bayyana.

Za a buga wasan kusa da na karshe ne a ranar Laraba 7 ga watan Fabrairu da karfe 6 na yamma.

Najeriya Vs Angola: Tinubu ya gana da Super Eagles

Awanni gabanin karawarta da Angola, tawagar Najeriya ta gana da shugaban kasa Bola Tinubu ta hanyar bidiyon kai tsaye.

An ruwaito cewa Tinubu ya karfafi guiwar tawagar domin samun nasara a wasan da za su kara da Angola don zuwa wasan na kusa da karshe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel