AFCON 2023: Tinubu Ya Yi Magana da Tawagar Super Eagles Gabanin Karawa da Angola

AFCON 2023: Tinubu Ya Yi Magana da Tawagar Super Eagles Gabanin Karawa da Angola

  • Shugaba Tinubu ya samu zantawa da tawagar Najeriya ta Super Eagles awanni kadan kafin karawarsu da kasar Angola
  • A yau Juma’a ne da misalin karfe 6 na yamma za a fara wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON)
  • An ruwaito Seyi, ɗan Tinubu, ya wallafa bidiyon shugaban da ke magana da tawagar ta hanyar bidiyon kai tsaye

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya karfafi guiwar tawagar Super Eagles a yayin da take shirin buga wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON) da Angola.

A cikin shafinsa na Instagram, Seyi, ɗan Tinubu, ya wallafa bidiyon shugaban da ke magana da tawagar ta hanyar bidiyon kai tsaye.

Kara karanta wannan

Ahmed Musa Ya Ba Super Eagles Sirrin Doke Kasar Angola a Gasar AFCON 2023

Tinubu ya yi magana da Super Eagles
Tinubu ya gana da Super Eagles kafin karawarsu da Angola. Hoto: @NGSuperEagles, @Dolusegun16
Asali: Twitter

Tinubu ya zanta da tawagar Super Eagles

A cikin faifan bidiyo da aka soke muryarsa, Tinubu na sanye da rigar Super Eagles yayin da yake magana da tawagar ta hanyar kwamfuta a gabansa, rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mista Bola Tinubu ya yi wa Super Eagles jawabi kafin wasan AFCON da Angola."

- A cewar Seyi Tinubu.

A yau Juma’a ne da misalin karfe 6 na yamma Super Eagles za su kara da Angola a filin wasa na Felix Houphouet-Boigny da ke birnin Abidjan na kasar Ivory Coast.

Stanley Nwabali zai tsare ragar Najeriya

Jaridar The Cable ta ruwaito cewar Stanley Nwabali ne zai fara tsare ragar Najeriya a wasan na yau.

Dan wasan mai shekaru 27 ya ji rauni ne a wasan zagaye na biyu da Kamaru, kuma ya yi gwajin lafiyarsa a makare don buga wasa da Angola.

Kara karanta wannan

AFCON: Ganduje ya bi sahun Kwankwaso inda ya tura sako ga tawagar Super Eagles, bayanai sun fito

Jose Peseiro, babban kocin Super Eagles, shi ma ya tsaya kan tsarinsa na gargajiya na 3-4-3 tare da William Troost-Ekong, Semi Ajayi, da Calvin Bassey don kare Nwabali.

AFCON 2023: Kwankwaso ya jinjinawa wa Super Eagles

A wani labarin, jagoran jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya jinjinawa tawagar Najeriya ta Super Eagles kan kokarin da suke yi a gasar AFCON 2023.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter, Kwankwaso ya ce yana fatan tawagar Najeriya za ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka ta wannan shekarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel