Ronaldo, Benzema Da Zaratan 'Yan Wasa 6 Da Suka Tsallake Barcelona Zuwa Real Madrid Bayan Siyan Arda Guler
- Manyan kungiyoyin kwallon kafa a Spain, Real Madrid da Barcelona sun sha gwagwarmaya wurin siyan 'yan wasa
- Real Madrid a bangarensu sun sha rasa damarmaki na siyan 'yan wasa da suke zuwa kungiyar Barcelona
- Legit.ng ta tattaro muku jerin shahararrun 'yan wasa da suka tsallake Barcelona zuwa Madrid bayan siyan Guler
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sanar da siyan matashin dan kwallo, Arda Guler a ranar Alhamis 6 ga watan Yuli.
Dan wasan mai shekaru 18 ana sa ran shahararsa anan gaba yayin ake kwatanta shi da shahararren dan kwallon nan Lionel Messi.
Dan wasan ya rattaba hannu a kwantiragin shekaru shida a Bernabeu bayan damar kungiyar Barcelona na siyan dan wasan ta subuce.
Manyan kungiyoyin kwallon kafa guda biyu a Spain, Real Madrid da Barcelona sun sha gasa akan zaratan 'yan wasa kafin daga bisani dan wasan ya zabi wacce tafi kwanta masa a rai.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jerin 'yan wasan da suka tsallake Barcelona zuwa Real Nadrid
Legit.ng ta bangaren wasanni ta tattaro muku jerin 'yan wasan da suka zabi Real Madrid akan Barcelona.
1. Dani Ceballos
Dani Ceballos ya ki zuwa Barcelona inda ya ce ya gwammace ya buga wa Madrid a kakar 2017 akan kudi €18m.
Dan wasan a farkon wancar kaka ya rasa matakin buga wasa inda ya yi dana sanin zaban Madrid akan Barcelona.
Daga bisani ya samu gurbin buga wasa a kungiyar bayan wasu watanni kadan a kungiyar.
2. David Beckham
Bayan rasa dama da Manchester United ra yi na kofin FA a 2003 a hannun Arsenal, ana hasashen David Beckham zai koma Barcelona da taka leda, cewar rahotanni.
Shugaban kungiyar Barcelona John Laporta ya yi yakin neman zaben zama shugaban kasa a wancan lokacin, inda ya yi alkawarin zuba makudan kudade don siyo Beckham amma hakan bai yiyu ba.
David Beckham ya fusata bayan Laporta ya yi amfani da shi a siyasa don cin ma burinsa, makwanni kadan Beckham ya rattaba hannu a kungiyar Real Madrid da ke adawa da Barcelona.
3. Isco
Isco ya samu karbuwa daga manyan kungiyoyi biyu a Spain, Madrid da Barcelona bayan nuna bajinta da Malaga ta yi a kakar shekarar 2013.
Isco ya zabi Madrid akan Barcelona duk da cewa shi magoyin bayan Barcelona ne tun yana karami.
Wannan ba shine karon farko ba da Isco ke kin Barcelona, a shekarar 2010 ma ya ki amincewa da taka leda a Barcelona saboda ba ya son koyan yaren Cataloniya.
4. Marco Asensio
Asensio ya bayyana yadda ya rage kadan ya rattaba hannu don buga wa kungiyar Barcelona kwallo lokacin da yake Mallorca.
Dan asalin kasar Spain, Asensio a karshe ya bijirewa Barcelona tare da saka hannu a kwantiragi da Madrid akan kudi €4m.
5. Vinicius Junior
Vinicius ya saka hannu wa kungiyar Real Madrid lokacin yana da shekaru 16 akan kudi €40m.
Bayan rasa damar dauko Neymar da Madrid suka yi, sun yi nasarar wafce Vinicius daga Barcelona wanda suka yi imanin cewa shine gatan kasar Brazil nan gaba.
Vinicius Junior ya ce ya zabi Madrid ne akan Barcelona saboda ya na son buga tambola a kungiyar da tafi kowacce a duniya.
6. Karim Benzema
Benzema ya bayyana yadda ya zabi Madrid kungiyar da tun yana karami ya ke sha'awar buga mata wasa akan Barcelona.
Madrid sun sayi Benzema ne akan kudi €35 bayan ya sha kwallaye 54 a kaka biyu da ya yi a kungiyar kwallon kafa ta Lyon.
Benzema ya ce duk da Madrid ce zabinsa, amma ba su kadai ne ke zawarcin shi ba a wancan lokaci.
7. Mesut Ozil
Ozil ya zabi ya buga tambola a Madrid bayan taka muhimmiyar rawa a gasar cin kofin duniya a 2010 da aka yi a Afirka ta Kudu.
Kungiyoyi da dama na zawarcin dan wasan, na gaba gaba su ne Barcelona da Madrid.
Ozil shima ya gwammace ya zabi Madrid akan Barcelona bayan kocin Real Madrid a wancan lokaci, Jose Mourinho ya yi bakin kokarinsa don ganin ya jawo shi kungiyar.
8. Cristiano Ronaldo
Barcelona na sha'awar siyan Ronaldo a 2009 amma basu nuna wata alamu na son mallakar dan wasan a hukumance ba.
Lokacin da yake buga tambola a Manchester United, kocinsa Sir Alex Ferguson ya zabi Barcelona akan Madrid wa dan wasan yayin da yake shirin barin kungiyar.
Rahotanni sun ce Ronaldo da kansa ya matsa sai da ya rattaba hannu a Madrid madadin Barcelona.
Wannan sauya sheka ta Ronaldo zuwa Madrid shi ya kawo gasa tsakaninsa da Lionel Messi na tsawon shekaru 10.
Ronaldo Na 1, Messi Na 2: Forbes Ta Fitar Da Jerin 'Yan Wasan Da Suka Fi Dibar Daloli
A wani labarin, Forbes ta fitar da jerin 'yan wasan da suka fi kowa dibar kudade a shekarar 2023.
Bayan Ya Shafe Watanni 4 a Otel Din Alfarma, Matashi Ya Ajiye Cak Din Miliyan 12 Na Bogi Sannan Ya Tsere
Jimillar kudaden ba a lissafa da alawus da kuma haraji na 'yan wasan ba kamar yadda mujallar Amurka ta bayyana.
Mujallar ta ce jerin 'yan wasan guda 10 akalla suna diban $1.11bn ba tare da haraji ko sallaman wakili ba.
Asali: Legit.ng