Ronaldo Na 1 Messi Na 2: Forbes Ta Fitar Da Jerin Sunayen 'Yan Wasan Da Suka Fi Kwashe Daloli a 2023

Ronaldo Na 1 Messi Na 2: Forbes Ta Fitar Da Jerin Sunayen 'Yan Wasan Da Suka Fi Kwashe Daloli a 2023

  • Mujallar Forbes ta fitar da jadawalin sunayen ‘yan wasan motsa jiki da suka fi diban kudade a mabanbantan wasanni
  • Rahoton ta bayyan ‘yan wasa 10 da suka fi kowa diban albashi a harkan wasanninsu daban-daban
  • Messi, Ronaldo da Mbappe su ne sahun gaba a jerin sunayen da suka fi diban makudan kudade a harkan kwallon kafa.

Mujallar Forbes ta Amurka ta fitar jerin ýan wasan da suka fi samun kudi ta shekarar 2023.

Jerin sunayen ya bayyana albashin ‘yan wasan ba tare da haraji ko alawus ba da kuma tallace-tallace.

Ronaldo/Messi
Ronaldo na 1 Messi na 2: Forbes ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasan da suka fi kwashe daloli a 2023
Asali: Facebook

Mujallar ta bayyana cewa ‘yan wasa 10 da aka fitar a jerin rahoton suna diban akalla $1.11bn ba tare da haraji ko sallamar wakili ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Gobarar titi: Gwamnati ta raba wa wadanda aka kwaso daga Sudan N100k, katin N25k da data 1.5GB

Rahoton ya fayyace $20m da kuma 12% daga shekarar da ta gabata na $990m, sannan karin 5% na $1.6bn da aka samu a shekarar 2018.

‘Yan wasan kwallon kafa ta Amurka su suka mamaye jerin sunayen ‘yan wasan motsa jiki .

Jerin sunayen ya kunshi ‘yan wasan motsa jiki 10, da ‘yan wasan kwallon kafa da kuma kwallon kwando su suka mamaye jerin sunayen, in da na gaba-gaba ke dauke da ‘yan wasan kwallon kafa 3.

Ronaldo ya fi kowa

Bayan ya sauya sheka zuwa kasar Saudi Arabia, Cristiano Ronaldo shi ne akan gaba da kudaden shiga akalla $36m, sakamakon albashi na $75m.

Abokin hamayyarsa, Lionel Messi shi ne ke biye da akalla makudan kudaden shiga da yakai $130m.

Na ukun su shi ne jajirtaccen dan kwallon kafan Faransa, Kylian Mbappe da zunzurutun kudi $120m.

Ga jerin jadawalin sunayen da ‘yan wasan ke samu:

Kara karanta wannan

Jam’iyyun Adawa Sun Yi Taro, An Tsara Yadda Za a Yaki ‘Yan Takaran APC a Majalisa

  • Cristiano Ronaldo (kwallon kafa - Portugal) - $136m
  • Lionel Messi (kwallon kafa - Argentina) - $130m
  • Kylian Mbappe (kwallon kafa - Faransa) - $120m
  • LeBron James (kwallon kwando - Amurka) - $119.5m
  • Canelo Alvarez (dambe - Mexico) - $110m
  • Dustin Johnson (kwallon sanda na gof - Amurka) - $107m
  • Phil Mickelson (kwallon sanda na gof - Amurka) - $106m
  • Stephen Curry (kwallon kwando - Amurka) - $100.4m
  • Roger Federer (Tennis - Switzerland) - $95.1m
  • Kevin Durant (kwallon kwando - Amurka) - $89.1m

Mahaifiyar Hakimi Ta Ce Bata San da Danta Ya Sanya Sunanta a Kadarorinsa Ba

A wani labarin, Mahaifiyar dan wasan kwallon kafan Maroko da PSG Achraf Hakimi, Saida Mouh ta yi martani game da jita-jitan cewa danta ta maka sunanta kan dukkan kadarorinsa.

A cewar Saida, bata san da hakan ba, kuma bata shirya hakan tare dan nata ba, rahoton jaridar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel